Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 23.05.2020

Taskar Guibi: 23.05.2020

246
0
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, wajen wadanda suka ga jinjirin watan Shawwal jiya da almuru zuwa dare, yau daya ga watan Shawwal wato yau Sallah karama, sai bangaren Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na Uku da ya sanar cewa gobe lahadi ce daya ga watan Shawwal, akwai cikon azumi na talatin ke nan yau asabar, gobe lahadi ce Sallah.
Da farko dai jiya da yamma ina shirin hawa labarun karfe shida da kwata na yamma na DITV/Rediyon Alheri nake magana da wani cewa bana na dauko lissafin watannin musulunci tiryan-tiryan babu wanda ya kalubalanceni kamar yadda aka sha yi mun a shekarun baya, musamman idan ana neman jinjirin watan Ramadan ko na Shawwal. Ashe da sauran rina a kaba. Da daddare na ga wasu a soshiyal midiya wato fesbuk na ta bayanin sun ga wata, wasu ma suka rantse da idonsu sun gani. Har Masarautar Zazzau ma ta fitar da tata sanarwar cewa ta ga wata, azumi ya kare yau Sallah. Ita kuma Fadar Mai Alfarmar Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwar za a cika azumi talatin, saboda babu wata sanarwar da ta samu ta an ga wata. Wannan ya haifar da rudani. Wanne ne ba wanne ne ba? Ni dai na san wasu ma tun shekaranjiya ko jiya suka yi sallarsu ta Idi. Na kuma san ko an ga wata jiya ko ba a gan shi ba, wasu yau za su yi Sallah, wasu kuma sai gobe. Saura da me? Allah Ya mana maganin wannan rudani, Ya hada kan Musulmi Amin.
Na biyu jama’a na ta mun korafin rubutun da nake yi na labaru ya cika tsawo da yawa, mutanen yanzun ba sa iya jurewa karanta rubutun da ya cika tsawo da yawa. Kuma shi ya sa nakan kokarta wajen takaita kowanne labari, inda nakan bar kowanne labari a sakin layi daya kawai. Amma zan ci gaba da kokarin ganin ina takaitawa, don burina shi ne a karanta.
1. Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari ya ce a cikin gida zai yi tasa salkar Idin tare da iyalansa, tare da cewa ya hutar da duk wani da ke son zuwa masa yawon Sallah ko gaisuwar Sallah, saboda kauce wa harbuwa da kwaronabairos.
2. Wasu ma’aikatan lafiya na jihar Kaduna sun soma yajin aiki a jiya juma’a a kan yanke musu albashin watan Afrilu da na Mayu, duk da gargadin da gwamna ya yi cewa wanda ya tafi yajin aiki to ya kori kansa daga aiki.
3. Gwamnatin Tarayya ta ce a watanni uku na farkon shekarar nan, ta yi asarar kudin shiga naira biliyan ashirin da biyar saboda kwaronabairos.
4. Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari ya sanya hannu a kan wata doka tasa da ta sakar wa bangaren majalisun dokoki na jiha da bangaren shari’a na jihohi marar cin gashin kai, ta yadda za su iya kashe kudadensu ba sai sun jira gwamnati ba.
5. Wasu ‘yan bindiga sun auka Abuja suka kashe mutum uku da fashin kaya.
6. Jiya a dandalina na wasaf an tafka muhawara mai zafin gaske tsakanin masu goyon bayan sanarwar da Sarkin Musulmi ya bayar ta lahadi ce Sallah, da wadanda ba sa goyon bayan sanarwar tasa.
7. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 245 ne a jihohi kamar haka:
Legas 131
Jigawa 16
Ogun 13
Barno 12
Kaduna 9
Oyo 9
Ribas 9
Ebonyi 9
Kano 8
Kwara 7
Katsina 5
Akwa Ibom 3
Sakkwato 3
Bauci 2
Yobe 2
Anambra 1
Gwambe 1
Neja 1
Ondo 1
Filato 1
Abuja 1
Bayelsa 1
Da ke nuna zuwa jiya da daddaren kowacce jiha tana da alkalumma kamar haka:
Legas 3224
Kano 883
Abuja 447
Katsina 308
Barno 247
Jigawa 241
Bauci 230
Oyo 199
Ogun 196
Kaduna 179
Gwambe 145
Edo 144
Sakkwato 116
Ribas 89
Zamfara 76
Kwara 73
Filato 71
Yobe 47
Oshun 42
Nasarawa 38
Kabbi 32
Delta 31
Adamawa 27
Neja 23
Ondo 23
Ebonyi 22
Akwa Ibom 21
Ekiti 20
Taraba 18
Inugu 16
Bayelsa 8
Abiya 7
Imo 7
Anambra 6
Binuwai 5
Kogi 0
Kuros Ribas 0
Jimillar wadanda suka harbu 7,261
Jimillar wadanda suka warke 2,007
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 227
Ragowar da suke jinya 5,027
Wadanda yau ce Sallah a wajensu, a yi Sallah lafiya. Wadanda kuma gobe ce Sallah, a yi sahur lafiya, a yini lafiya, a yi buda baki lafiya.
Af! Akwai labarun da yawa, kamar na sifetan ‘yan sanda a kan tabbatar da tsaro, da shirin da Nijeriya ke yi na daukaka kara a kan hukuncin da kotun Ingila ta yanke a kan badakalar man Malabu, da ta kai Shell da ENI, da nadin sabon shugaban NECO, da gwamna Ortom da ya sassauta dokar kulle a jihar Binuwai don samun damar ibada, da Canisawan nan da aka ce sun zo warkar da kwarona ashe sun zo kwadago ne a wani kamfani da bai da basaba da kwarona.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply