Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 23.06.2020

Taskar Guibi: 23.06.2020

293
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, daya ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban Majalisae Dattawa Ahmad Lawal shi ma ya janyo hankalin shugabannin bangarorin tsaro na kasar nan, ko su dage wajen tabbatar da tsaro ko a fatattake su.

2. Gwamnatin Tarayya ta bukaci shugaban ofishin jakadanci na Ghana da ke Nijeriya, ya je ya mata bayani a kan ginin da aka rushe a ofishin jakadanci na Nijeriya da ke Accra Ghana.

3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC har da shugabannin majalisun dokoki na tarayya don gano bakin zaren sake dinke jam’iyyar ta zama tsintsaya daya madaurinki guda.

4. Ba a samu damar ci gaba da shari’ar Wadume da wasu mutum shida ba a jiya saboda alkalin da ke yin shari’ar bai ji dadin jikinsa ba.

5. Osagie Ize-Iyamu aka zaba a zaben fid-da-gwani na wanda zai tsaya wa APC takarar gwamna a jihar Edo. Sai dai Giodam ya rubuta wa hukumar zabe ta kasa cewa ba a gudanar da zaben fid-da-gwani na jam’iyyar APC ba tukuna, an dage sai nan gaba.

6. ‘Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare a jihar Zamfara inda suka kashe mutum a kalla ashirin da daya, wasu kuma suka kai hari yankin Dandume da ke jihar Katsina suka kashe mutum a kalla uku, sai ‘yan kungiyar Boko Haram da suka kai hari sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori, da ke jihar Barno inda suka jidi kayan abinci. An bayyana cewa daga watan jiya na Mayu zuwa yau, ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai hari ya fi sau dari daya, da ya sanya akwai ‘yan Nijeriya su fiye da miliyan uku daga yankin Barno da ke gudun hijira, sai kusan dubu talatin da aka kashe, sannan akwai kananan hukumomi biyar da babu tabbacin tsaronsu, da yawancin wadanda ke cikinsu sun yi gudun hijira zuwa Nijar da Kamaru.

7. Sojojin sama sun ce sun kai farmaki Bula Belo Ngoske suka lalata mafaka na ‘yan kungiyar Boko Haram.

8. ‘Yan sanda sun kama mutum shida da ke da nasaba da fashin da aka yi a banki na Isanlu a jihar Kogi kwanakin baya.

9. Edwin Clerk da wasu, sun bukaci shugaban kasa ya biya su naira biliyan hamsin saboda zargin nuna bambanci ko karkata bangare guda na kasar nan wajen nade-naden mukamansa.

10. Gwamnatin Tarayya ta bukaci masu makarantu da ke zaman kansu, su je wajen Babban Bankin Nijeriya ko sa samu kudaden da za su ci gaba da biyan malamansu albashi. Don akwai korafe-korafen tunda aka rufe makarantu saboda kwaronabairos, makarantun suka kasa biyan malamansu albashi. Haka ma makarantun Islamiyya.

11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya, da kusan wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

12. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwarona su 675 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 288
Oyo 76
Ribas 56
Delta 31
Ebonyi 30
Gwambe 28
Ondo 20
Kaduna 20
Kwara 20
Ogun 17
Abuja 16
Edo 13
Abiya 10
Nasarawa 9
Imo 9
Bayelsa 8
Barno 8
Katsina 8
Sakkwato 3
Bauci 3
Filato 3

Zuwa jiyan mutum dubu ashirin, da dari tara da goma sha tara suka harbu a kasar nan, dubu bakwai da dari da guda tara suka warke, sai mutum dari biyar da ashirin da biyar da suka riga mu gidan gaskiya, sai guda dubu goma sha uku, da dari biyu da tamanin da biyar da ke jinya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu gaskiya a jita-jitar da ake ta barbadawa cewa ta killace jihar Kaduna gabadayanta. Ta kuma ce babu hannunta a cire limamin masallacin juma’a na ‘yan lilo da ke Tudun Wadar Kaduna.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply