Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 23.12.2020

Taskar Guibi: 23.12.2020

487
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Laraba, takwas ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Disamba, shekarar 2020.

1. Jibi take kirsimeti kodayake ban ji Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutu ba ko ta shafa’a ne?

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoto daga kwamitinsa na sa ido a kan kwaronabairos PTF a takaice, inda ya kara wa kwamitin wa’adin wata uku don ganin yadda sabuwar cutar za ta kasance.

3. Gwamnatin Tarayya ta bukaci ma’aikatanta na gwamnati da ke matakin albashi na goma sha biyu zuwa kasa, su tsahirta da zuwa aiki, su dinga gudanar da aikin daga gida, nan da mako biyar a ga yadda za ta kasance da sabuwar cutar kwaronabairos.

4. Sojojin sun ce babu gaskiya a zargin da Gwamna Zulum ya musu cewa suna sa shinge suna karbar taro-sisi-kwandala, su da ‘yan sanda, maimakon kare rayukan mutanen jihar Barno.

5. Kungiyar gwamnonin Nijeriya ta je ta yi wa Gwamnan Jihar Katsina Masari kaico-kaicon abin da ya auku na yara ‘yan makarantar sakandare ta Kankara, tare da alkawarin za su nuna da gaske suke yi wajen shawo kan matsaloli musamman kidinafin da sauransu.

6. Gwamnonin jihohin tsakiyar Nijeriya sun taru a Makurdi ta jihar Binuwai domin lalubo bakin zaren magance matsalar tsaro irin su kidinafin da sauransu da ke addabar jihohin.

7. Gwamnatin Tarayya da malaman jami’a da ke yajin aíki, za su kuma taron tattauna yadda malaman za su janye yajin aikin dalibai su koma makaranta.

8. Daliban jami’a ‘yan mata da suka gaji da zaman jiran ranar komawa makaranta, na ta yin aure abin su, wanda ya sa in aka lura auren ya karu a wuraren karshen shekarar nan. Don na ga ‘yan matan na ta rubutawa a soshiyal midiya cewa su fa tunda ba makaranta aure suke so.

9. Jihar Kogi ta tsere wa Legas bangaren masu zuwa su zuba jari, a watanni uku na karshen shekarar nan. Ga wani can yana cewa Yahya Bello ba ruwansa da kwaronabairos shi ya sa ake tururuwa jiharsa zuba jari.

10. Wasu kidinafas sun kashe wani dan sanda da ya yi kokarin ceton wasu mutum biyu da kidinafas din suka yi kidinafin a kauyen Bosuwa da ke Maigatari a jihar Jigawa.

11. A jihar Kaduna an kashe mutum bakwai, aka sace uku a wani sabon hari.

12. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami”o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin sun kusan cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

13. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari tun lokacin yakin neman zabe. Na idan sun zabe shi zai gyara musu gadar. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
.
14. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 999 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 416
Legas 324
Kaduna 68
Filato 42
Kwara 32
Kano 24
Gwambe 12
Sakkwato 12
Yobe 12
Akwa Ibom 11
Bayelsa 10
Ribas 7
Bauci 7
Ogun 6
Oyo 5
Edo 4
Taraba 4
Jugawa 1
Jimilkar da suka harbu 79,789
Jimillar da suka warke 68,879
Jimillar da ke jinya 9,679
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,231
***Yau ana ta yayin 9 a alkaluman.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina talakan Nijeriya? Ka tuna tsine wa su Jonathan da Namadi Sambo har da kafirta duk magoya bayansu a lokacin yakin neman zaben 2015 da ka yi? Ka manta har jifarsu da kona gidajen magoya bayansu ka yi?
Ka lura a yanzun Jonathan ke wakiltar shugaban kasa a sabgogi daban-daban na kasashen waje? Ko a jiya na ga Jonathan a fadar shugaban kasa ya je ya isar da sakon aikensa da shugaban kasa ya yi kasar Gambiya. Shi ma Namadi Sambo ya je fadar shugaban kasa jiya don isar da sakon aikensa da shugaban kasa ya yi Nijar.

Af! Yanzun karfe hudu da minti 16 na asubah.

Na yi nan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply