Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 24.02.2021

Taskar Guibi: 24.02.2021

71
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha biyu ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Fabrairu, na shekarar 2021.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsarin tsaron sararin watayawa da sadarwa ta intanet na Nijeriya na shekarar 2021, da ake kira da turancin Ingilishi 2021 Cyber Security Policy and Strategy.

2. Majalisar Dattawa ta amince da nadin da Shugaban Kasa ya yi wa su Buratai na zama Jakadun kasar nan a kasashe-daban da za a tura su, da yin kira a gare su, su kare martaba da al’adun kasar nan a can.

3. Majalisar Wakilai ta amince da nadin da Shugaban Kasa ya yi wa su Attahiru a matsayin sabbin hafsoshin tsaro na kasar nan.

4. Kasa da wa’adin sa’a 48 da Attahirun ya ba sojojinsu su je su fatattaki ‘yan Boko Haram da suka kwace Marte a hannunsu, sojojin nasa sun fatattake su, ‘yan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu. Sai dai ana murnar bako ya tafi ashe yana labe a bayan gida, sai ga su ‘yan Boko Haram din sun kai hari kusa da Jami’ar Maiduguri, suka kashe mutum goma, 47 na asibiti, har Gwamna Zulum ya leka asibitin da suke. Sai dai nan ma sojojin Attahiru ba su yi kasa a gwiwa ba, sun nausa can da makamai suka mayar wa da ‘yan Boko Haram martani.

5. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce aikin da ya sanya a gaba na ceto ‘yan Nijeriya su miliyan dari daga talauci, ba karamin aiki ba ne.

6. Gwamnoni sun je yi wa Gwamnan jihar Neja Bello kaico-kaicon abin da ya auku a jihar na kidinafin ‘yan makarantar Kagara.

7. Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya ce tattaunawa da ‘yan fashin daji ba alamu ne na gazawa ba.

8. Gwamnatin Jihar Oyo ta ba da umarnin a sake bude kasuwar Sasa ta Ibadan da Yarbawa suka yi wa Hausawa rotse a kwanakin baya. Ahmed Lawan Shugaban Majalisar Dattawa, ya zargi gwamnonin yarbawa da hura wutar rikicin kabilanci a jihohinsu.

9. Masu raba wa jihohi alkaluman kwaronabairos, jiya sun raba kwarona 571 a jihohi kamar haka:

Legas 170
Ogun 64
Abuja 45
Kwara 34
Abiya 32
Inugu 32
Kano 25
Oyo 22
Ondo 21
Ribas 19
Kaduna 19
Binuwai 18
Bayelsa 12
Kabbi 12
Nasarawa 11
Akwa Ibom 9
Delta 8
Ekiti 6
Neja 5
Bauci 3
Imo 3

Jimillar da aka raba wa Nijeriya zuwa jiya, 153,187
Jimillar da aka raba wa wadanda aka ce sun warke 129,943
Jimillar da aka ware wa majinyata 21,370
Jimillar da aka ware wa matattu 1,874

10. Ma’aikatan Kwalejojin Foliteknik, da na Kwalejojin Ilimi, da na Jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi sun cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

i. Af! A rubutuna na jiya, na yi batun mun hadu da daya daga cikin shugabannin karamar hukumar Kudan, a kan gyaran gadar Guibi. Ga martanin da daya daga cikin idon garin Guibi, Abubakar Yahya ya yi a rubutun na jiya kamar haka:

“Af– To a gaskiya abin takaici a ce ba a yi mana alkawarin gyaran gadar nan ba.Domin anyi hakan a gaba na a gaban Shenagun Zazzau, a gaban dagacin Mazara. Waye mai musun nan?
Sannan a ce dankwangila na bin miliyan biyar, to wadannan kudade ba aikin gadar nan ba ne, to nawa ne kudin aikin gaba daya?
Kuma abin kaico ne ace wai ba a yi mana alkawari ba.Kenan ba za a yi mana komai ba?In har Shugaba zai iya bude baki ya fadi haka,to bakinsa ya fi karfinsa.Kuma ina da tabbacin ba Jaja ba ne. Na san ya iya magana amma wannan ai rainin hankali ne”

ii. Af ! Jiya da maraice ina sauraron BBC Hausa, sai na ji tsohon abokin aikina, da muka yi aiki a sashen labaru da al’amuran yau da kullum na rediyon jihar Kaduna, a wuraren shekarar 1994 kafin ya ware zuwa BBC, wato Abba Ahmed Abdullahi, ya fassara SWITCH OVER FROM ANALOGUE TO DIGITAL, da SAUYAWA DAGA DUNGU ZUWA YATSU.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply