Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 24.06.2020

Taskar Guibi: 24.06.2020

297
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, biyu ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen galitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo – Addo ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari ta wayar tarho, yana ba shi hakuri da nemar gafara da afuwar rushe wani gini na ma’aikata da aka yi a harabar babban ofishin jakadanci na Nijeriya da ke Ghana. Tunda farko shugaban majalisar wakilai ya ce wannan tamkar hari ne kasar Ghana ta kawo wa Nijeriya.

2. An yi zargin ‘yan sanda sun dode sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja, sai dai ‘yan sanda sun ce ba dode sakatariyar suka yi ba, alamu suka gani na rashin jituwa ta sa suka girke karin jami’ansu a wajen.

3. Sanata Ali Ndume ya amince ya tsaya wa Abdulrashid Maina don ba da belinsa. Da farko kotu ta bukaci sai sanatoci biyu kuma da naira biliyan daya, a matsayin sharuddan ba da belinsa, a yanzun kotu ta sassauta sanata daya da naura miliyan biyar. Ana zargin Maina da wawure wasu makudan kudi na fansho, shi kuma ya ce atabau wasu ne da ke da hannu wajen wawurar kudin suka masa kage da sharri.

4. Kotu ta hana APC ko hukumar zabe hana dukkan ‘yan takaran da aka wanke tsayawa takarar zaben-fid-da gwani na gwamna na jihar Edo. Shi ma gwamna Obaseki kotu ta amince ya shiga sahun ‘yan takarar fid-da-gwani kodayake akwai wani cikinsu da ya garzaya kotu cewa akwai sharuddan da Obaseki bai cika ba.

5. Kasar Saudiya ta ce a bana maniyyata na kasarta ne kawai za su sauke farali ban da sauran na kasashen duniya saboda kwaronabairos.

6. ‘Yan sanda sun ceto wasu ma’aikatan wani kamfanin shinkafa su dari uku da ke Kano, da aka garkame su a cikin kamfanin ba shiga ba fita suna ta sirfar aiki.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

8. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 452 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 209
Oyo 67
Delta 37
Ogun 36
Abuja 22
Abiya 20
Inugu 16
Bauci 15
Kaduna 8
Ondo 8
Oshun 7
Imo 3
Binuwai 3
Barno 1

Jiya da shekaranjiya ban ga jihar Kano a jerin sabbin harbuwa kamar yadda ba a barin jihar Kaduna a baya ba?

Jimillar wadanda suka harbu a kasar nan zuwa jiya da daddare mutum dubu ashirin, da dari uku da saba’in da daya, sai wadanda suka warke guda dubu bakwai da dari uku da talatin da takwas, sai wadanda suka riga mu gidan gaskiya, mutum dari biyar da talatin da uku. Wadanda suka yi saure suke jinya, mutum dubu goma sha biyu, da dari biyar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016 wata rana mai kamar ta yau, shekara hudu baya, na yi wani rubutu a wannan dandalina nawa na fesbuk, da asubah, da fesbuk suka turo mun a matsayin waiwaye. Ga wannan rubutu na kwafo shi don na ga ya zo daidai da halin da ake ciki a yau kamar haka:

‘Allah Ya saukar da daya daga cikin ni’imominSa ga dan Adam wato ruwan sama. Mu a nan tun jiya muke shan ruwan sama har zuwa jijjifin asubahin yau. Allah Kenan Buwayi Gagara misali. Mai kyauta da kari ba gori ba bambanci ba sharri ba kazafi ba bakin ciki ba sa ido. Allah Mai yin yadda Ya so a lokacin da Ya so a inda Ya so. Mai hura rai da numfashi, Ya raya Ya maka arziki na lafiya da dukiya. Ya ba ka hanci da ido da kafa da siffa mai kyau don ka ji dadin bauta masa ba gori. Ya maka wajen fitsari da kashi don kada ka takura. Ya maka sutura da sanya kauna a zuciyarka ba ta kiyayya da mugunta da zalunci ba. Ya yi mu kasa-kasa jinsi-jinsi don fahimtar juna ba kiyayya ba. To don Allah wadannan ba su ishe mu ishara mu rabu da mutum ba mu koma ga Ubangiji? Me mutum zai maka? Shi ma ta kansa yake yi. Shekaranjiya na ji Dr Shek Gumi na cewa a bude kofofi a saki arziki a kasar nan a fawwala komai a hannun Ubangiji Allah Ne mai yin komai. Za a fita daga cikin kangin da ake ciki muddin aka yi imani da Shi. Allah ba don halinmu ba Ka kara mana ni’ima da imani Ka yafe mana kurakuranmu Amin. Ka ba mu falalar wannan juma’a da wannan wata mai alfarma Amin. Allah Kai Ka san makiyanmu da ba sa kaunar ci gabanmu Kai Ka san yadda za Ka mana da su, Kar Ka ba su sa’a a kanmu Amin’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply