Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 24.11.2020

Taskar Guibi: 24.11.2020

427
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, takwas ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 56 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Kaduna 18
Legas 6
Filato 5
Kano 3
Kwara 2
Yobe 2
Ekiti 1
Neja 1
Ribas 1
Jimillar da suka harbu 66,439
Jimillar da suka warke 62,241
Jimillar da ke jinya 3,030
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,168

2. Shekaranjiya da daddare wasu kidinafas sun je daya daga cikin gidajen ma’aikata na jami’ar E.BI.YU. /A.B.U. da ke Samarun Zariya, suka yi kidinafin wani malami da matarsa da diyarsa. Da yake an sanar da ”yan sandan kwantar da tarzoma, nan take suka kai dauki aka yi harbe-harbe, da kidinafas suka lura za a fi karfinsu, suka bar matar da diyar suka tafi da shi mijin. Har na ji wasu na cewa su kidinafas ba su san yawanci malaman jami’a rabonsu da albashi tun watan Maris na wannan shekarar ba ne?
Bayanai na nuna kidinafas sun sako wanda suka yi kidinafin a kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya.

3. An yi kidinafin wani Baba Wuro dan uwan wani Minista mai ci.

4. Wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar sojoji bawai da JTF daya, a hanyarsu ta kai kayayyakin agaji wajen ‘yan gudun hijira a jihar Barno, ashe ‘yan kungiyar sun bisne bom a hanyar.

5. Wata kotu ta sa a tsare mata Sanata Ndume a gidan yari na Kuje saboda shi ya tsaya wa Abdulrasheed Maina beli, ga shi ya kasa gabatar da Maina, ana batun Maina ya gudu. Kotu na bukatar Ndume ya biya gwamnatin tarayya wata Naira Miliyan Dari Biyar ko sayar da kaddararsa don biyan kudin. Sai dai na ji wasu na korafin don me ba a yi wa Sanata Aberibe da ya tsaya wa Nnamdi Kanu, a karshe Kanun ya gudu haka ba, sai Sanata Ndume?

6. Ministar Kudi Zainab, ta ce a watanni uku na sabuwar shekarar 2021 da za a shiga, tattalin arzikin Nijeriya zai murmure daga RECESSION da ya shiga.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na Jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na cewa idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekarar da ke shirin kankama, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

8. A wajen tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, da Kungiyar Kwadago a kan karin kudin mai da na lantarki, shugabannin kwadagon sun fice daga wajen taron don nuna rashin gamsuwa da inda gwamnati ta dosa a wajen tattaunawar.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura, ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Shekara biyar ke nan da Allah Ya yi wa mutumina Ahmed Aja Gwarzo da Ahmed Usman rasuwa.

Ga rubutun da na yi a rana mai kamar ta yau, 24/11/2015 wato shekara biyar daidai:

“Allah Ya jikan Ahmed Usman da Ahmed Aja Gwarzo. Shi Ahmed Usman mun yi aiki tare da shi a kamfanin Newage Network a shekarar 2010. Shi kuwa Ahmed Aja Gwarzo da wuya ya ji an yi Hausar da ba ta dace ba a rediyo bai kira ni a waya ya shaida mun ba. Sannan duk juma’a sai ya sayi jaridar Leadership ta Hausa don karanta rubutun da na saba yi a shafin adabi. Yana buda shafin zai kira ni a waya ya ce ga rubutunka nan ina karantawa. Ni ma kuma kusan duk Lahadi shirinsa na wasa kwakwalwa ba ya wuce ni. Lahadi da ta gabata da na ji Muhammad Lawal Kaya ya soma gabatar da shirin da bayanin Aja Gwarzo ba lafiya, sai na kira wayar Aja Gwarzo, na ji ya amsa mun da kyar sai jikina ya yi sanyi. Ya ce “Guibi ne?” Na amsa masa ni ne. Ya ce “ina asibiti” Da yake na san yakan kai ‘ya’yansa asibitin Biba, sai na tambaye shi “Wanne asibiti? Na Biba?” Ya ce “Asibitin Dutse” Na ce masa “Allah Ya ba ka lafiya sai gobe da safe Idan za ni ofis zan biyo” Ya ce ya gode. Iyali da yake sun san yadda yake yawan waiwayata a waya suka tambaye ni na ce musu Aja Gwarzo ba lafiya muryarsa ta canza. Da safe Allah Bai ba ni ikon biyawa ba don gaskiya na shafa’a. Na dawo gida daga Birnin Yero wuraren karfe daya na rana iyalina suka ce sun ji sanarwar rasuwar mutumina Ahmed Aja Gwarzo. Allah Ya jikansu da rahama, ya yafe musu kurakuransu, mu da muka yi saura Allah Ka sa mu cika da kyau da imani Amin”

Yanzun karfe hudu da minti goma sha hudu na asubah.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply