Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 24.12.2020

Taskar Guibi: 24.12.2020

368
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, tara ga watan Jimada Ula/Awwal, shekakarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fitayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Disamba, na 2020.

1. Gobe take kirsimeti, kuma tuni Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun goben, Juma’a, da kuma litinin, sai kuma ranar daya ga watan sabuwar shekarar 2021, ita ma hutu ce

2. Malaman jami’a sun sanar da sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe wata tara suna yi. Dakatarwa da sharadin idan gwamnati ta saba musu alkawari, za su ci gaba da yaji ba tare da sun ba da wani notis ko gargadi ba. Sun ce a yanzun ya rage ga shugabanni jami’o’i da gwamnati su sanar da dalabai ranar da za su koma makaranta, su dai malamai daga yau sun koma aiki. Na ma ga wasu jami’o’i irin su ta Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-ma a jihar Katsina sun fitar da sanarwar an ci gaba da karatu daga yau.

3. Ana ta muhawara a kan kalaman da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi cewa Allah ne kadai Zai iya magance matsalar da ke tattare da kan iyakar Nijeriya da Nijar. Inda wasu ke cewa gazawa ce karara shugaban kasa ke nunawa.

4. A hanyar Okene zuwa Lakwaja wata mota ta yi hadari mutum goma sha biyar suka riga mu gidan gaskiya.

5. A jihar Kwara wata tankar mai da ke mugun gudu ta kwace ta fadi, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum shida, gidaje fiye da talatin suka kone, da shaguna fiye da arba’in.

6. A hanyar Kaduna zuwa Abuja, wata motar daukar kaya, saboda mugun gudu da rashin kyawon hanyar, ta kwace wa direban ta fadi, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum goma sha biyu, ashirin da biyar suka ji rauni.

7. Kidinafas sun je Minjibir ta jihar Kano, an ce gaskiya jami’an tsaro sun fafata da su, duk da haka sun tafi da wani mai hali a garin.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi da aka dade da biyan sauran ma’aikata.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar ta Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya dauka na gyara musu gada, da a lokacin yakin neman zabe, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa ba gyara musu ba.

10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 1,133 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 397
Abuja 357
Kaduna 81
Filato 63
Katsina 46
Sakkwata 32
Oyo 28
Ogun 21
Kano 19
Ribas 18
Oshun 13
Edo 12
Neja 12
Bayelsa 11
Bauci 8
Jigawa 2
Ondo 2
Jimillar da suka harbu 80,922
Jimillar da suka warke 69,274
Jimillar da ke jinya 10,412
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,236.

11. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa na karshe a wannan shekarar, har an fitar da wasu ayyuka.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga rahoton da aka turo mun jiya da daddare daga yankin Giwa ta jihar Kaduna:

” Abinda ya faru yau kenan a garin Galadimawa da wasu mahara suka Kawo hari makamancin Abinda ya faru a Kidandan inda harin yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu/uku da raunata wasu da kuma Tarawatsa kasuwa kasancewar yau kasuwar garin keci.

Bugu da kari sum kona Babban mota ta daukan kaya wato Daf/Triller da wata karama ta hawa akan hanyar Gwar-gwaje zuwa Birnin Gwari a nan kusa da Garin Kidandan dake yankin Giwa ta Yamma Kaduna state
Haka zalika sum kuma kewaye garin da manyan Makamai suna ta harbe-harbe. Ta ko inna a fili babu wani jamiin tsaro da ya Kawo wani dauki har ya zuwa wnn. Lokaci..

Daya daga cikin Wanda suka kashe shine Commander JTF na Yankin Iyatawa, Kidandan Ward, Giwa LGA Kaduna”

Af!! Wasu na zargin ana biyata ne a kullum nake rubuta alkaluman kwarobabairos. To ni ba wanda ya taba ba ni ko kwandala. Amma idan akwai wanda zai mun hanya a dinga kason kudin da ni, to ba matsala.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply