Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 25.05.2020

Taskar Guibi: 25.05.2020

152
0
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, biyu ga watan Shawwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhamnad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Mayu na shekarar dubu biyu da ashirin.
1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da tasa sallar Idin jiya shi da iyalansa a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan sun idar ya karfafa wa musulmi da sauran ‘yan Nijeriya gwiwar komai zai daidai, kuma a ci gaba da yi wa kasar nan addu’a da fatan alheri. Sai dai na ji wasu suna radar cewa shin duk a Nijeriya mutum biyu ne kawai aka yafewa sa takunkumi? Wato Baba Buhari da Aisha Buhari? Sun ce ba su taba ganin Baba Buhari ko Aisha Buhari waninsu ya taba sa takunkumi ba, ko dai shi da ita, ta Yahaya Bello gwamnan jihar Kogi da na Kuros Ribas duk sun gano kwaronabairos bula ce kawai? In ji wani don ni bakina da goro sai na furzar.
2. A jiya an yi sallar Idi a Kano, da Katsina, da Kuros Ribas, da Bayelsa da wasu jihohi nan da can da aka ce duk da dokar hana sallar Idin a filayen Idi, a wasu kauyukansu an yi.
3. Matan talakawa da ke cikin garin Kaduna na tururuwa gidajen da suka ga suna da manyan kyaure suna barar garin rogo ko tsaki da za su ci da yara. Misali mu a Kinkinau kusan da safe, da rana da kuma yamma, matan sun maye gurbin almajiran da muka saba ji da gani suna allaziwahidun. In dai kana da get babba to sai ka tanadi kayan abincin da za ka rika ba su.Ga wani can yana rada cewa gwamnati ta kulle su da mazansu, kuma sai dai su ji labarin wai gwamnati na rabon kayan abinci. Suka ce anya ba a dauki alhakin talaka ba kuwa?
4. Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN ta yi kira ga gwamnati ta kyale jama’a su dinga zuwa masallatai da coci-coci.
5. Gwamnatin jihar Bauci ta ce tana kashe naira dubu daya da dari biyar a kowanne kwanon abinci da take ba mai jinyar kwaronabairos a jihar. Wato kowanne na cin abincin naira dubu hudu da dari biyar ke nan a kullum? Ga wani can yana radar an zo wajen.
6. Jiya an yi mace-mace a cikin garin Kaduna. Saboda shekaranjiya Allah Ya yi wa Hassan Kabido fitaccen dan wasan kwaikwayon nan musamman Jatau Na Albarkawa na rediyon jihar Kaduna rasuwa. Mun je jana’iza makabartar Bashama da ke Tudun Wadar Kaduna jiya da safe cikin ruwan sama. Muna makabartar zuwa barinmu an ce an kai gawa ta kusan ashirin. Ga wani can yana radar… Sshhhhhh! Na katse shi. Allah Ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya Amin.
7. Sallah ta wuce ina labarin dilin-dilin ne? Don ma’aikatan gwamnatin tarayya sun ce da ma ba su sa a ka ba in ji barawon hula kodayake wadancan masu bakin magana sun ce sun samu kafin Sallah. Ina ma’aikatan foliteknik da na kwalejojin ilimi da ke ta jiran ariyas fiye da shekara daya ke nan? Ina malaman jami’o’i da yawancinsu rabon da su ga albashi tun watan Janairu? Ina aka kwana a sa-in-sa da ake ta yi tsakanin babban akanta da malaman jami’a a kan IPPIS?
8. Natanyahu a kotun Urshalima saboda zarginsa da bakin cin rashawa.
9. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci, akwai mutane guda 313 sabbi da suka harbu da kwaronabairos a jihohi kamar haka:
Legas 148
Abuja 36
Ribas 27
Edo 19
Kano 13
Ogun 12
Ebonyi 11
Nasarawa 8
Delta 8
Oyo 7
Filato 6
Kaduna 5
Kwara 4
Akwa Ibom 3
Bayelsa 3
Neja 2
Anambra 1
Kowacce jiha da ke kasar nan har da Abuja a jiya da daddare tana da alkaluma kamar haka:
Legas 3,505
Kano 896
Abuja 505
Katsina 308
Barno 250
Jigawa 241
Oyo 240
Bauci 232
Ogun 231
Edo 191
Kaduna 189
Gwambe 145
Ribas 116
Sakkwato 116
Filato 83
Kwara 79
Zamfara 76
Yobe 47
Nasarawa 46
Oshun 42
Delta 39
Ebonyi 33
Kabbi 32
Neja 28
Adamawa 27
Akwa Ibom 24
Ondo 23
Ekiti 20
Inugu 18
Taraba 18
Bayelsa 11
Anambra 9
Abiya 7
Imo 7
Binuwai 5
Kogi 0
Kuros Ribas 0
Jimillar wadanda suka harbu 7,839
Jimillar wadanda suka warke 2.263
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 226
Wadanda suka yi saura suna jinya 5,350
Mu ci gaba da shagulgulan Sallah lafiya.
Af! Ina jiran kajin Sallah amma gaskiya na fi son kajin Hausa ba na son na aggiri. In ka fito za ka kawo mun kajin jami’an tsaro suka tare ka, ka fada musu za ka kai wa Malam Guibi kaji ne. Za su kyale ka.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply