Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.05.2020

Taskar Guibi: 26.05.2020

112
0

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga manoma su kara himma wajen noma abinci mai tarin yawa a bana, don wadata gida Nijeriya da abinci, saboda gwamnati ba ta da kudin da za ta iya sayo abinci daga kasashen waje.

2. Jihohin da suka amince aka yi sallar Idi a filayen Idi da aka saba, akwai Kano, da Sakkwato, da Nasarawa, da Yobe, da Bayelsa da sauran jihohi da na ambata a rubutuna na jiya.

3. An yi wata gobara a sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar Barno, mutum biyu suka riga mu gidan gaskiya, muhalli guda dubu daya da dari shida da goma sha uku ya salwanta.

4. Sojoji sun ce sun kashe ‘yan bindiga fiye da dari biyu a jihar Zamfara da ta Katsina, haka nan sun ce sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP a yankin Barno masu yawan gaske.

5. Nepa sun yi halin nasu. An dai san me nake nufi kodayake akwai saukin zafi saboda an yi ruwan sama, sauro ne dai matan ke ta gada, mazan ke ta buga kwallo harbarta-mati.

6. Nijeriya ta ci tarar wani jirgi na Ingila saboda saba wa wasu dokoki na Nijeriya.

7. An kwaso ‘yan Nijeriya su sittin da tara daga kasar Labanan, hamsin daga cikinsu ‘yan mata ne da aka yi safararsu ci-rani, sauran goma sha taran suna karakainar neman hanyar dawowa.

8. A jihar Kano an yi wa fursunoni dari uku ahuwa.

9. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya da rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan, na nan suna ci gaba da korafi. Haka nan ma’aikatan kwalejojin ilimi da na kwalejojin foliteknik sun ce sun haura shekara daya da wata daya a yanzun haka suna zaman jiran ariyas. Wasu kuma sun soma cigiyar dilin-dilin na Mayu.

10. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO a takaice ta dakatar da gwajin Kulorakwin wajen warkar da kwaronabairos saboda wasu dalilai na kare lafiya kamar yadda ta ce.

11. Amurka ta haramta wa ‘yan kasar Birazil zuwa Amurka saboda kamarin da cutar kwaronabairos ta musu a can.

12. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai mutane 229 sabbin harbuwa da kwaronabairos a jihohi kamar haka:

Legas 90
Katsina 27
Imo 26
Kano 23
Abuja 14
Filato 12
Ogun 9
Delta 7
Barno 5
Ribas 5
Oyo 4
Gwambe 3
Oshun 2
Anambra 1
Bayelsa 1

Kowacce jiha zuwa jiya da daddare tana da alkaluma kanar haka:

Legas 3595
Kano 919
Abuja 519
Katsina 335
Barno 255
Oyo 244
Jigawa 241
Ogun 240
Bauci 232
Edo 191
Kaduna 189
Gwambe 148
Ribas 121
Sakkwato 116
Filato 95
Kwara 79
Zamfara 76
Yobe 47
Delta 46
Nasarawa 46
Oshun 44
Ebonyi 33
Imo 33
Kabbi 33
Neja 28
Adamawa 27
Akwa Ibom 24
Ondo 23
Ekiti 20
Inugu 18
Taraba 18
Bayelsa 12
Anambra 10
Abiya 7
Binuwai 5
Kogi 0
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 8,068
Jimillar wadanda suka warke 2,311
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 233
Jimillar wadanda ke jinya 5,524

Mu wayi gari lafiya, wadanda ke cikin kulle kuma mu fito kulle lafiya.

Af! A rubutuna na jiya wani ma’aikacin karamar hukumar Kaduna ta Arewa Muataju Ahmad wanda malami ne da ke koyarwa ya yi korafi a kan hakkokinsu daban-daban kamar haka:
” Dr,muna sun kataimaka kamar yanda Allah ya taimakeka. kan batun hakkokin ma’aikatan local govement , kamar yanda kasabayi . hakkokinsu kuwa shine, misali, malumman primary wadanda suke aiki da wadanda sukabari, albashinsu na watanni da na hutu ba maganansu, ba rana . saboda haka munga kokarinka yasa kataimaka domin sanin inda aka kwana. Allah yataima kemu bakidaya Ameen. Dr barka da sallah Allah yamai maita mana Ameen, wassalam”

Da na ga ya yi korafin na kira shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, ya mun bayanin in dai batun malamai ne, to ya je SUBEB. A wadanda suka ba mai korafin shawara, a rubutun nawa na jiya, har da wani Murtala Makera, kamar haka:

“Muataju Ahmad Bari Inbaka Labari Akan Abinda Yafaru Damu Akan Albashin Mu, a Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu,Muna Bin Bashin Albashin Wata Goma Sha Shida Mu Biyar Akayi Mana Rinton Na Wata Biyu, Akace Wata Goma Sha Hudu Za Abiya Mu,Kafin Nan Bama Cikin Ma’aikatar Da Aka Sallama, Ama Sai Aka Kawo Yan Gatan Gwamnati Akace Sune Za ai Retaining Mu Mudakata Akan Haka Mun Rubuta Petition Na Dauka Da Kaina Na Kai Gidan Gwamnati Office Din Gwamna Akai Mun Acknowledge.Naje Office Din Komishinan Kananan Hukumomi Nama Na Kai Komishina Ya Kiramu Muka Zauna Da Wadan Da Akace Su Zauci Gaba Da Aikin Mu, Kowa Ya Kawo Hujojin Shi Da Appointment Letter Aka Duba, Nan Take Komishina Ya Fusata Yace Mune Muke Kan Aiki, Yabada Umurnin Aje A Rubutawa Local Government Sun Biya Mu Hakokin Mu, Saida Na Kwana Ashirin Da Hudu Ina Suntiri Bani Ministary Bani Local Government, Bari In Takaita Maka Wasu Abubuwan Dana Gani Bazasu Fadu Anan Ba, Wallahi Akan Hakokin Mu Har Daga Fadar.Shugaban Kasa Wani Baban Jami’i Yasa Baki Ama Har Kwanar Gobe Ba Abamu Takardan Sallama Daga Aiki Ba Kuma Ba Abiyamu Hakokin Mu Ba, Bare Aci Gaba Da Biyan Mu Albashi Kuma Munada Appointment Letter a Hanun Mu, Inadai a Jihar Kaduna Ne Sai Dai Kuyi Hakuri Kuci Gaba Da Adu’o’in Allah Ya Bulo Maku Da Wasu Hayoyin Na Alheri Inda Zaku Samu Abin Rufin Asiri, Duk Abinda Kaga Kananan Hukumomi Nayi Dasanin Gwamna, Allah Ya Kawo Mana Mafita Baki Daya”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply