Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.06.2020

Taskar Guibi: 26.06.2020

684
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, hudu ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Kwamitin zartaswa/koli na jam’iyyar APC ya rusa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar tare da kafa wani kwamiti na riko karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe Mai Malla Buni, da ba shi wata shida ya daidaita komai, kuma shugaban kasa Buhari da ya jagoranci zaman ya bukaci duk wani mai wata kara a kotu ya janyeta.

2. Tsohon gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi da shi ne bayan dakatar da Oshiomhole aka ba rikon jam’iyyar sai dai aka ce ba shi da lafiya, ya riga mu gidan gaskiya jiya.

3. Mutun uku da ke takarar fid-da-gwani da gwamna Obaseka a PDP sun hakura sun janye sun bar masa.

4. Gwamnatin Ghana za ta gina wa Nijeriya ginin da wasu suka rushe mata a babban ofishin jakadancinta da ke Accra Ghana. Goeffrey ministan harkokin waje ya ce har da laifin jami’an Nijeriya domin tun a shekarar dubu biyu suka sayi filin suka biya, suka ki bibiyar takardun wajen, da kuma izinin gini.

5. Da yake ‘yan bindiga sun ci gaba da kashe jama’a a jihar Katsina da ta Zamfara, kisa na baya-bayan nan shi ne wasu kauyuka biyu a Dan Musa ta jihar Katsina da maharan suka je da karfe biyun dare su fiye da dari biyu, suka kashe na kashewa har da mata da dan sanda, da jikkata na jikkatawa suka jidi abinci da dabbobi suka yi gaba abin su, kungiyar hada kan mutanen Arewa da hadin gwiwar malamai da limamai da fastoci, sun kira taron manema labaru a Kaduna, suna rokon gwamnati da hukumomin tsaro su yi wa Allah su magance kashe ‘yan Arewa da ‘yan bindiga ke ta yi.

6. Wasu talakawa sun ce da ma kurari Baba Buhari ya yi wa shugabannin tsaron kasar nan, su sun san ba abin da zai iya musu, shi ya sa suka bari aka ci gaba da kashe talakan Arewa duk da barazanar da ya yi.

7. Babban Bankin Duniya ya ce faduwar farashin mai da cutar kwaronabairos sun yi wa tattalin arzikin kasar nan taron dangi za su tika shi da kasa, su masa kayen da bai taba ganin irinsa ba tun shekarun 1980.

8. Masu wutar lantarki na Kaduna sun ce a zauna cikin shiri domin daga daya ga watan gobe, za a kara wa talaka biyan kudin zama a duhu. Wato kudin da talaka ke biya na zama a duhu ya yi arha da yawa.

9. A karshen makon nan kwamitin shugaban kasa kan cutar kwaronabairos zai mika wa shugaban kasa rahotonsa, kuma babu mamaki jiragen sama su dawo da zirga-zirga ta cikin gida, a makon gobe.

10. An maido da ‘yan Nijeriya da ke Afirka ta kudu su dari biyu gida, an killace su duk da gwajin da aka musu kafin kwaso su na nuna ba su harbu da kwarona ba.

11. ‘Yan sanda a Dubai sun saki bidiyon wani dan damfara dan Nijeriya Hushpuppi da zuwa yanzun ya damfari mutum miliyan daya da dubu dari tara, ga tulin durhami har guda biliyan daya da rabi, da kaddara da aka kama shi da su malala gashin tunkiya.

12. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata uku ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka ma wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

13. Yau ashirin da shida an soma dakon dilin-dilin na wannan watan tun jiya, tunda da ma dadadden alkawari ne da tun hawan wannan gwamnatin ta yi cewa albashin ba zai dinga wuce ashirin da biyar ba a biya ba.

14. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 594 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 159
Delta 106
Ondo 44
Abuja 34
Edo 34
Oyo 33
Kaduna 33
Inugu 28
Katsina 25
Imo 22
Adamawa 15
Ogun 12
Oshun 11
Abiya 8
Ribas 6
Nasarawa 5
Bauci 5
Neja 5
Kabbi 4
Ekiti 3
Filato 1
Taraba 1

Jimillar wadanda suka harbu a kasar nan zuwa jiya da daddare, mutum dubu ashirin da biyu, da dari shida da goma sha hudu, wadanda suka warke mutum dubu bakwai da dari takwas da ashirin da biyu, sai wadanda suka riga mu gidan gaskiya, mutum dari biyar da arba’in da tara, sai wadanda ke jinya, mutum dubu goma sha hudu, da dari biyu da arba’in da uku.

15. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a don duba shafukan dandalina na labarun da na rubuta daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis. A kuma leka Taskar Guibi da ke dandalin jaridar Dutsen Kura Communication Limited, da kuma shafukan sharhina na kullum a jaridar Muryar ‘Yanci ta Libati rediyo da talabijin, da Kainuwa, da sauran dinbin wurare da dandali da shafuka, da kungiyoyi da daidaikun jama’a, gidajen rediyo da talabijin da a kullum ke kai rubutun labarun nawa ko’ina a duniya. Duk ina godiya.

Mu yi juma’a lafiya.

Af! Jiya na shiga mota bas daga Kasuwar Bacci zuwa UTC/Yutisi a cikin garin Kaduna. Naira arba’in zuwa hamsin na saba biya kodayake kwana biyu ban hau ba. Na tambayi kwandasta nawa ya ce naira dari. Na tambayi dalili ya ce saboda kwarona. Na tambaya kwarona kamar ya? Ya ce yanzun maimakon misali mutum hudu, biyu suke diba. Na duba cikin motar na ga cike motar take babu wata tazara yadda suka saba diba a muna biyan naira hamsin, haka suke cunkusa mutane a muna biyan dari. Saboda haka abin zai yi wa talaka yawa. An rage kudin mai bai gani a kasa ba, sai ma ninka masa kudin mota da aka yi, aka fake da kwarona ana cutarsa. Lantarki a cuce shi. Can kauyuka ana ta kashe shi da kidinafin dinsa, ya shiga mota a damfare shi. Inda yake kasa kaya an wartake shi. Kaico talakan Nijeriya ya ga arkane!

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply