Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.09.2020

Taskar Guibi: 26.09.2020

251
0

Assalamu alaikum barkannmu da asubahin asabar, takwas ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Satumba shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Gwamnatin Tarayya ta kuma garzayawa kotu don neman ta hana kungiyoyin kwadago na kasar nan tsindima yajin aiki jibi litinin idan Allah Ya kai mu, don nuna rashin yarda da karin kudin zama a duhu da na mai da gwamnatin tarayyar ta yi. Su kungiyoyin ma’aikata sun nanata ko ma ina gwamnatin tarayya za ta garzaya don hana su, sai sun yi. Kungiyoyin ma’aiatan shari’a na kasar nan, JUSUN da kungiyoyin ma’aikatan bankuna da na Inshora da sauran cibiyoyin kudi, sun ce sun kosa jibi ta yi su yi yajin aiki.

2. Gwamnan jihar Edo Obaseki ya je fadar shugaban kasa ya yi wa shugaban kasa Buhari godiya a kan nasarar da ya sake samu aka kuma zabarsa gwamnan jihar. Buhari ya ce ya ga bai dace a ce wanda bai ji bai gani ba an wahalar da shi. Shi ya sa ya umarci shugaban ‘yan sanda ya tabbatar an yi zaben gaskiya a zaben na jihar Edo.

3. An kai wa ayarin gwamnan jihar Barno Zulum farmaki a Baga, aka kashe masa sojoji uku da ‘yan sanda takwas.

4. An kashe sojoji uku aka ji wa da dama rauni a lokacin da suka yi kokarin dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai wani kauye da ke Faskari ta jihar Katsina.

5. Amurka ta ba Nijeriya dala miliyan biyu da ‘yan kai don gudanar da bincike a kan kwaronabairos a jihohin Inugu da Nasarawa da Gwambe.

6. Majalisar Wakilai ta sanya wata na’urar laturonik da a yanzun an daina jin muryar kowa wajen nuna goyon baya ko akasin haka ga duk wani kudiri sai dai kowa ya dinga danna ra’ayinsa ta na’urar da ke gabansa, da kuma rage makudan kudin da ake kashewa wajen amfani da takarda a zaman majalisar.

7. Garba Shehu na kokarin musanta bayanin da Amaechi ya yi cewa gwamatin tarayya za ta yi titin dogo daga Kano zuwa Maradi, shigen musunta bayanin da Lai ya yi cewa kayan abinci na arha. Inda Zainab ta ce bayaninsa ba daidai ba ne abinci na tsada.

8. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki ga ambaliya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

9. Za a bude makarantu na firamare da na sakandare ranar 12 ga watan gobe a jihar Bauci.

10. An rantsar da Bah Ndaw a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Mali. Ya dau alkawarin mika mulki nan da wata 18 ga gwamnatin farar hula da za a zaba.

11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a ma wata da watanni ba albashi.

12. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 213 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 51
Filato 51
Abuja 29
Ribas 18
Ondo 12
Oyo 9
Oshun 8
Gwambe 7
Ogun 7
Kaduna 5
Inugu 4
Edo 3
Jigawa 3
Kano 3
Binuwai 1
Delta 1
Sakkwato 1

Jimillar da suka harbu 58,062
Jimillar da suka warke 49,606
Jimillar da ke jinya 7,353
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,103

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wani ke tambayata ra’ayina a kan yajin aikin da kungiyoyin kwadago za su wayi gari da shi jibi a kan karin kudin zama a duhu da na mai da gwamnatin tarayya ta yi. To gaskiya ra’ayina da kungiyoyin kwadago sun dan tsahirta ma’aikata sun ji dilin-dilin wato albashi tukuna.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply