Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.10.2020

Taskar Guibi: 26.10.2020

358
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, tara ga wtatan Rabi’ul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Oktoba na shekarar 2020.

1. Gwamnatin Tarayya ta ce akwai wata naira biliyan ashirin da biyar da za ta bayar, ta matasa ce, don magance tashin hankali na matasan.

2. Jama’a na ci gaba da wasoson kayan abinci duk inda suka samu labari an adana kayan abinci, kuma na baya-bayan nan ita ce Yola. Suka fasa sito uku da har ta kai ga gwamna Umar Fintiri ya sa dokar hana walwala ta sa’a 24 a fadin jihar Adamawa.

3. A jihar Kaduna kuwa da yau za a shiga yini na biyu da dokar hana walwalar ta sa’a 24 da gwamnatin jihar ta sa sakamakon balle sito na hukumar kula da inganci abinci da magunguna NAFDAC, da kuma wani sito na wani kamfanin abinci, gwamnatin jihar ta yi gargadin magungunan da jama’a suka jida, wasu sun tashi aiki sun zama guba, wasu ba su da inganci hadari ne shan su, kayan abincin kuma na kamfanin an sa wa waken da sauransu maganin kwari da idan mutum ya ci yana iya mutuwa. Gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce ta adana daya kayan abincin ne, tunanin za a sake sa dokar kulle don kwarona sai a raba wa jama’a, sai ga shi jama’a sun wawushe.

4. Haka ma a Abuja jiya jama’ a suka leka sito-sito na NAFDAC guda biyu suka sa wawa, har da katifu da kwanfutoci da man gyada.

5. A Legas kuwa su Gbajabiamila da dukkan gwamnonin jihohin Yarbawa da Ministocinsu ne, suka yi cincirindo a can don jajanta wa gwamna da jama’ar jihar abin da ya faru. An rage dokar hana walwala ta sa’a 24 ta koma daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na asubah.

6. Kungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduha ta ce ba ta ji dadin yadda a jihar Kaduna gwamnatin na jiran ta ji kiri ne ta kakaba wa jama’a dokar kulle ba. Ta ce ina ma laifi ta sa a yankunan da abin ya faru ba jihar gabadaya ba?

7. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kaucewa cewa uffan a kan Lekki ne har sai ya gama samun cikakken bayanin hakikanin abin da ya faru.

8. Wasu sun kai farmaki gidan tsohon shugaban majalisar wakilai Dogara da ke Jos.

9. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

10. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu suna zaman jira ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya

Af! Jiya akwai iyayen dalibai da suka kira ni a waya ce wa an ba ‘ya’yan nasu Jinga/Assignment su kawo kalmomi masu gaba shida-shida. To ga uku:

A ram ba da kwal le
Ma ku ru run ci ya
Ku lin ku lif fi ta

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply