Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.11.2020

Taskar Guibi: 26.11.2020

429
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, goma ga watan Rabi’ul Sani,shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fitayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. daidai da ashirin da shida ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1. Wasu ma’aikata sun soma korafin yau 26, ya kamata a soma jin dilim-dilin na watan nan daga yanzun.

2. ‘Yan Arewa daga sama zuwa kasa na ci gaba da korafi a kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a yankin Arewa.

3. Jama’a na ci gaba da korafin ga shi an kara kudin wuta, ga ba wutar. Talaka na ci gaba da biyan kudin zama a duhu, kuma duhun sai kara tsada yake yi.

4. Talakan Nijeriya, na ci gaba da korafin rayuwar sai kara tsada take yi, komai ya yi tsada.

5. ‘ Yan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan tsadar mai, tsadar da ta sanya komai ya yi tsada.

6. Gamaiyar kungiyoyin matasan Arewa, ta ci gaba da korafin saboda Sanata Ndume mutumin Arewa ne shi ya sa kotu ta tsare shi tun Litinin da ta gabata a kan Maina, har ma kotun ke shirin sayar masa da kaddarorinsa. Matasan suka ce ai ga su Aberibe nan da suka tsaya wa Kanu, har Kanu ya gudu ya kuma ci gaba da tsine wa Nijeriya da shugabanninta da buga gangar yaki, ba abin da aka yi wa wadanda suka tsaya masa, sai dan Arewa, da yake shi ne ba shi da gata a wannan gwamnatin. A yau kotu za ta saurari bukatar ba da belin Sanata Ndumen.

7. Talaka musamman na Arewa, na ci gaba da korafi a kan rufe bodojin kasar nan, kodayake gwamnati na shirin bude su nan gaba kadan, inda ake shirin mika wa shugaban kasa rahoton kwamitin da ya kafa a kan rufewar.

8. Dan Majalisar Wakilai daga jihar Kaduna na ci gaba da korafi a kan yadda kidinafas ke damun jami’ar E.BI.YU Samarun Zariya, har ya kawo shawarar a samar da kan iyaka, da ofishin ‘yan sanda da bataliyar soja a jami’ar.

9. ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Birtaniya, na ci gaba da korafi a kan zargin jami’an tsaro na amfani da makaman yakin da har da ita Birtaniya ke tallafa wa a ba Nijeriya, ke kashe jama’a da makaman, zargi na baya-baya nan shi ne na Lekki. Birtaniya ta yi barazanar takunkumi, sai dai Gwamnatin Nijeriya na kokarin wanke kanta wajen Birtaniya.

10. ‘Yan Majalisar Dattawa na ci gaba da korafi a kan yadda kidinafas ke iya amfani da waya, su yi ciniki har a biya su kudin fansa da waya, ba tare da an gano su ba. Saboda haka suka nemi Ministan Sadarwa Pantami ya je ya musu bayani, saboda sun ce ba su gane ba an yi yamma da kare.

11. Daliban jami’a na Nijeriya, na ci gaba da korafin sun gaji da zaman gida, iyayensu da marikansu, su ma suna ta korafi.

12. ‘Yan PDP na jihar Adamawa na ci gaba da korafin Sanata Elisha Abbo ya cika wa rigarsa iska ya fice daga PDP ya koma APC.

13. Lauyan Maina na ci gaba da korafin Maina ba ya biyansa kudin aikin da yake masa, saboda yaka ya janye daga yi masa aikin lauyanci.

14. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

15. Pele fitaccen dan wasan Birazil, na ci gaba da korafin Diego Maradona fitaccen dan wasan Ajantina, ya mutu ya bar shi, sai dai ya ce bai cire ran za su ci gaba da buga kwallon kafa a lahira ba.

16. Mutanen kauyen Guibi, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

17. ‘Yan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan yadda alkaluman masu kwaronabairos ke karuwa, su kuma ba sa ganin masu cutar ko matattun a zahiri. Suka ce a jiya akwai sabbin harbuwa har 198 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 53
Legas 48
Ogun 40
Akwa Ibam 20
Bauci 9
Filato 8
Kaduna 5
Kano 4
Binuwai 3
Jigawa 3
Nasarawa 3
Edo 1
Kwara 1
Jimillar da suka harbu zuwa yanzun 66,806
Jimillar da suka warke, 62,493
Jimillar da ke jinya 3,144
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,169

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina shawagi a fesbuk sai na ga wata Salamatu Isah tana ci gaba da korafi a kan wasu matan aure kamar haka:

WALLAHI ! Wallahi !! Wallahi !!! Gaskiya dayace ya za ace mace da mijinta da yayanta amma taketa alfarmar auranta ta wulakanta auranta ta tozarta auranta da sunan taje wurin aiki SAI tayi sati bata kwana adakin mijinta yau ta kwana wurin wancan bayan tagamabin yan fira Anya wannan abun kadai be ishemu ya hanamu zaman lafiya akasar nanba yanzu munkai lokacin da Mara aurema tafi me aure kamunkai ga hakkin miji ga na iyaye gana yaya. Wallahi Tallahi yanzu matan aure sunfi karuwai karuwanci Allah ya bamu ikon gyarawa inba hakaba to mudaina zagin shuwa gabanni sakamakon mummuna mummuna ne inji Manzan Allah S.A.W

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply