Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 26.12.2020

Taskar Guibi: 26.12.2020

317
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, goma sha daya ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Disamba, na shekarar 2020.

1. Yau take boxing day da kiristoci ke raba kyaututtuka musamman a akwati wanda shi ne BOX din, da ke cikin bukukuwan kirsimeti da aka soma jiya.

2. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 712 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 388
Abuja 77
Kwara 39
Katsina 35
Bauci 33
Filato 22
Ogun 18
Akwa Ibom 16
Delta 13
Kaduna 12
Oshun 12
Yobe 11
Sakkwato 10
Kabbi 8
Inugu 6
Edo 5
Ondo 3
Neja 2
Kano 1
Oyo 1

*** Yau an yi wa jihar Kaduna kwauron alkaluma. Amna na san za a yi kara’i a alkaluman gobe.

Jimillar da suka harbu 82,747
Jimillar da suka warke 70,239
Jimillar da ke jinya 11,262
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,246

3. A albashin wata bibbyu da Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’a, daga watannin da suke bi, wasu sun samu wasu ba su samu ba har yanzun.

4. Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na ci gaba da korafin an yi kirsimeti ba dilin-dilin.

5. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin sun kusan cika shekara biyu suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.

6. Tana kasa tana dabo, a tsakanin malaman jami’a da sauran ma’aikata da ke aiki a jami’a a kan kudaden da malaman suka yi gwagwarmaya a kai, aka figarwa ma’aikatan kashi 25 daga ciki, suka ce su sun musu kadan sai dai a yi raba-daidai.

7. Kungiyar likitoci ta kasa ta ce a cikin mako guda, likitoci 20 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kwaronabairos.

8.Likitoci a jihar Taraba sun soma yajin aiki.

9. Wasu fusatattu a yankin karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna, sun yi kukan kura sun kashe ‘yan bindiga su shida, bayan ‘yan bindigan sun kashe musu mutum biyu.

10. Jama’a na nan suna ci gaba da korafi a kan biyan kudin zama a duhu a zamanin Baba Buhari mai gaskiya.

11. Wasu mutanen jihar Kaduna, na ci gaba da korafi a kan rushe-rushen gidajensu da kasuwanninsu.

12. Gwamna Zulum na jihar Barno ya roki a yi wa dakarun sa-kai na JTF da mafarauta da a halin yanzun haka, ana shagulgulan kirsimeti, su suna daji suna farautar ‘yan kungiyar Boko Haram, su ma ‘yan kungiyar ta Boko Haram suna farautarsu.

13. Gwamna Zulum na jihar Barno, ya roki a yi wa ‘yan gudun hijira da a lokacin nan da kowa ke gida yana bikin kirsimeti, su suna can suna layin abinci, ga sanyi, a sansanoni na ciki da wajen kasar nan.

14. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe, na gyara musu gada, don sun lura yana shirin sauka bai je ya cika musu alkawari ba.

15. A gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu, za a gudanar da zaben shugaban kasa na kasar Nijar.

16. Fafaroma Francis, ya bukaci a samar wa kowa da kowa alluran rigakafin kwaronabairos.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wasu malamai na ta ce-ce-ku-ce a kan yadda samarinmu ke tsallakewa su auro tsofaffin matan turawa, su ki auren dakwalen ‘yan uwansu ‘yan mata na gida. Ga wani martani da na ga wani Abubakar Isah ya rubuta:

Daga Abubakar Isah

“Idan kaje neman aure wajen naka suka hanaka ko su ka wulakantaka sai ka samu soyayya daga wurin wacce ba taka ba ashe bai kamata ka rike ta hannu bibiyu ba kuwa?
Yau ba malamin da shaharar sa ta kai daga matakin Jiha zuwa kasa baki daya har izuwa duniya baki daya da zaka je neman auren yarsa duk yadda yadda kai da haddar Alqur’ani ko ilimoma na addini hade da tarbiyya da zai dube ka ya baka yarsa ba tare da kana da abin duniya ba,muna kallo yau yaran malaman sun koma harka da yayan shuwagabanni ne masu rike da madafun iko bama takwarorin su yayan malamai ba.

Sannan a ina Allah ya hana auren Baturiya,ko kuma Ahlul kitabi? Ina Allah ya hana auren tsohuwa matukar ka aminta da ita kuma ta aminta da kai? Malaman ya kamata suyi duba kan abubuwa masu mahimmaci dasu ke damun al’umma a yau maimakon irin wadannan abubuwa da basu shafe su ba”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply