Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 27.05.2020

Taskar Guibi: 27.05.2020

158
0

1. Majalisar Dokoki ta Kasa za ta yi wani zama na gaggauwa gobe alhamis idan Allah Ya kai mu a kan kasafin kudin shekarar nan na 2020.

2. Majalisar Wakilai ta goyi bayan a binciki kamfanin raya yankin Neja Delta.

3. An yi wata gobara a kasuwar Delta.

4. Ana ta mutuwa a jihar Ribas da kokarin gano wacce cuta ce ke sanadiyyar mutuwarsu.

5. Gwamnan Anambra Willie Obiano ya ce ba zai ci gaba da tilasta kulle a jiharsa ba, don da za a yi bincike da kyau, za a gano yunwa ke ta kashe ‘yan Nijeriya a ‘yan kwanakin nan saboda tilasta musu kulle, ake yi wa kwaronabairos sharri ake cewa ita ce saboda an ga ba ta da gata.

6. Yau da gobe alhamis akwai walwalar tara kayan abinci a jihar Kaduna. Sai dai da an shiga watan gobe na Yuni, walwalar za ta zama ana yinta talata, da laraba, da alhamis, daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma. An yarda mai facin taya, da mai walda, da bakanike duk su fito a ranakun, haka wuraren dafa abinci, amma sai dai a saya a je gida a ci. Ba zirga-zirga daga birni zuwa birni, ko daga jiha-zuwa jiha don akwai kotuna-tafi-da-gidanka. Nan gaba kadan za a tattauna da wadanda abin ya shafa a kan sallah a masallatai da ibada a coci-coci.

7. Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce babu sauran wani yaro da zai bari yana yawon bara da sunan almajiranci a jihar Kaduna.

8. Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar korar ma’aikatan da ke fallasa asirin gwamnati.

9. Malaman wasu jami’o’i na gwamnatin tarayya, na nan suna ci gaba da dakon albashin watan Fabrairu, da na Maris, da na Afrilu, ga na Mayu. Su kuwa ma’aikatan kwalejojin Ilimi, da na kwalejojin foliteknik duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata daya ke nan suna jiran ariyas.

10. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbi da suka harbu da kwaronabairos su 276 a jihohi kamar haka:

Legas 161
Ribas 36
Edo 27
Kaduna 19
Nasarawa 10
Oyo 6
Kano 4
Delta 3
Ebonyi 3
Gwambe 2
Ogun 1
Ondo 1
Barno 1
Abiya 1
Bauci 1

Kowacce jiha da ke fadin kasar nan tana da:

Legas 3,756
Kano 923
Abuja 519
Katsina 335
Barno 256
Oyo 250
Jigawa 241
Ogun 241
Bauci 233
Edo 218
Kaduna 208
Ribas 157
Gwambe 150
Sakkwato 116
Filato 95
Nasarawa 56
Kwara 79
Zamfara 76
Delta 49
Yobe 47
Oshun 44
Ebonyi 36
Imo 33
Kabbi 32
Neja 28
Adamawa 27
Akwa Ibom 24
Ondo 24
Ekiti 20
Inugu 18
Taraba 18
Bayelsa 12
Anambra 10
Abiya 8
Binuwai 5
Kogi 0
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 8,344
Jimillar wadanda suka warke 2,385
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 249
Wadanda suka yi saura suna jinya 5,710

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na ji malaman firamare na karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na ta korafi a kan wasu hakkokinsu, shigen na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, da karamar hukumar Kaduna ta kudu. Kodayake shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya shaida mun cewa duk mai korafi ya je SUBEB.

Ga korafin mutumin na Kudan:

“Duk da akwai batutuwa cike da shafin yau amma dai batun malaman firamarennan ya ja hankalina,ya tunamin irin wannan al’amarin da ya faru a karamar hukumar Kudan
Karamar hukumar Kudan ta yi amfani da kudin hutun malaman suka biya ma’aikatan karamar hukuma a daidai lokacin da a ka biya malamai a sauran kananan hukumomi kudin hutun 2016 a 2018.
A da ana biyan malaman firamare kudin ne da kudin da ake cira daga albashinsu a duk wata.Su ko ma’aikatan karamar hukumar kyauta a ke basu.An ce har Gwamna ya sa baki amma har yanzu shiru ka ke ji…..
An fara biyan kudin hutun 2019.Shi wannan an raba kashi uku ne; kashin farko da na biyu an biya su (selectively)amma na uku su kuma ko oho.
Gaskiya kowanne malamin firamaren jihar Kaduna yana da labarin zantarwa.Abin takaicin mu jamaar gari mun ki fahimtar gazawar gwamnati a kan alkawurranta cewa sai sauran ma’aikata sun yi so inama suma malamai ne. Gaskiya dai wannan garin yana da nisa a yanzu.”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply