Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 27.11.2020

Taskar Guibi: 27.11.2020

375
0

Asalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, goma sha daya ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halita, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 169 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Kaduna 74
Abuja 42
Legas 17
Kano 8
Ogun 6
Oyo 6
Ribas 6
Ekiti 3
Bauci 3
Katsina 2
Delta 1
Ondo 1

Jimillar da suka harbu 66,974
Jimillar da suka warke 62,585
Jimillar da ke jinya 3,170
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,169

2. Gwamnatin Tarayya na nan tana ci gaba da tattaunawa da kungiyar kwadago a kan karin kudin mai da na wuta da ta yi wa talakan Nijeriya.

3. Tsohon shugaban mulkin soja Yakubu Gowon, ya ce babu gaskiya a zargin da aka masa a Majalisar Dokoki ta Birtaniya, cewa wai ya yi wa kudin Babban Bankin Nijeriya kwasar ganima.

4. Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Mahmud Yakubu ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi wa dokar zabe gyara.

5. Jiya na ga Babajide a shirin JOURNALISTS’ HANGOUT na tashar TVC, yana rantsuwa, yana sakewa cewa har yanzun a kwai wasu sassan kasar nan a hannun kungiyar Boko Haram.

6. Mahara da kidinafas na ci gaba da cin karensu babu babbaka a wasu sassan jihar Kaduna, da jihar Zamfara, inda su ma jami’an tsaro ke ta bayanin suna ta dama wa maharan lissafi. Mahara sun kai wa wasu kauyuka biyu da ke yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna hari.

7. Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin kasar nan, sun taru a jihar Adamawa don gano bakin zaren yadda za su bullo wa matsalar tsaro da ta addabi yankin ta bayan gida.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su gaura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

10. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, domin duba shafukana da ke kunshe da labarun da na kawo muku a dandalina na Soshiyal Midiya, daga Juma’ar da ta gabata zuwa jiya Alhamis.

Mu wayi gari lafiya, mu yi Juma’a lafiya.

Af! Yau Juma’a mu ci gaba da dagewa da addu’a. Su kuma Limamai da za su yi huduba yau a sallar Juma’a, su mayar da hankali ga jawo hankalin shugabanni na Arewa, su ji tsoron Allah, su tuna Allah Zai tambaye su, rayukan maza, da mata, da yara, da tsofaffi da suka bari suna ta salwanta da ko a jikinsu.

Af!!
Ga tsokacin da daya daga cikin wadanda suka bibiyi rubutuna na jiya ya yi:
“Malam Ishaq Idris Guibi Guibi, mutanen Jihar Kaduna masu motoci dake dauke da tsohuwar lamba, su na korafi a kan tilasta musu sayen sabuwar idan sun je sake sabunta takardun motocin su. Su ka ce idan sun je don sabunta takardun, sai a tambaya sabuwar lamba ce ko tsohuwa? Idan ka ce tsohuwa ce, sai a ce ba za a yi maka ba, sai dai ka sayi sabuwa a kan kudi N 33,000:00. Haka nan kuma, mutanen na ta kara korafin yadda Jami’an Kasteliya ke wa masu motoci kwanton bauna a hanyoyin cikin garin Kaduna. Da zaran sun mai motar dake da tsohuwar lamba, sai su yi ram, su kama shi. Nan take su rubuta maka takardar caji, ka je Barnawa ka biya kudin sabuwar lamba a kan N 33,000:00”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply