Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 28.09.2020

Taskar Guibi: 28.09.2020

298
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin 10 ga watan Safar shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 28 ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

KUNGIYAR KWADAGO TA DAKATAR DA NIYYARTA TA TSUNDIMA YAJIN AIKI YAU.

1. Yau ya kamata ma’aikata su tsundima cikin yajin aiki da zanga-zanga ta lumana a fadin kasar nan, don nuna kin amincewa da karin kudin zama a duhu, da karin kudin mai duka da gwamnatin tarayya ta yi. A kokarin hana yajin aikin, gwamnati ta garzaya kotu. Gwamnonin jihohi sun sa baki. Shugaban Majalidar Wakilai ya sa baki. Na ma ga gwamnan jihar Kaduna na barazana ga ma’aikatan jihar cewa duk wanda bai je aiki ba, ba shi da albashi. Kuma gwamnatin tarayya ta ga cewa da gaske ne za fa a tafi yajin aikin, ta kira shugabannin kungiyoyin fadar shugaban kasa, don tattaunawa da karfe bakwai na almurun jiya. A game da batun kotu kuwa kungiyar kwadago ta zargi gwamnatin tarayya ita ma da kin bin umarnin kotu na kada ta kara kudin lantarki. Labarin da ke ishe ni a yanzun karfe biyu da kusan rabi na dare da nake wannan rubutu kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ta yi niyyar yi. Gwamnatin tarayya ta janye karin kudin zama a duhu da ta yi.

2. Bayan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wa ayarin gwamna Zulum a ranar 25 ga watan nan har suka kashe masa sojoji da ‘yan sanda, da hukumar soja ta ce ita ta dakile harin, kuma bam da kungiyar ta bisne a hanyar da gwamnan zai bi, shi ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin, kungiyar ta kuma kai wa ayarin gwamnan hari a jiya da safe a kan hanyarsa ta Baga zuwa Maiduguri.

3. Ma’aikatan lafiya na tashoshin jiragen sama na kasar nan na korafin suna bin alawus na kwaronabairos na wata shida.

4. An rufe cibiyoyin killace masu kwaronabairos guda biyu da ke Abuja saboda karancin masu cutar.

5. Jihar Binuwai na fama da karancin ruwan sama har amfanin gona na ta mutuwa a gona, abin da manoman jihar suka ce ba su taba gani ba.

6. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, ga tsadar taki ga ambaliya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Har yau shiru.

8. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 126 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 30
Legas 24
Ribas 23
Ogun 13
Katsina 9
Filato 9
Ondo 6
Kaduna 4
Kwara 2
Imo 2
Bauci 1
Edo 1

Jimillar da suka harbu 58,324
Jimillar da suka warke 49,794
Jimillar da ke jinya 7,422
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,108

Mu wayi gari lafiya.

Af! A lokacin da ake ci gaba da dakon Gwamna El-Rufai ya zabi sabon sarkin Zazzau, na lura rabon Mallawa da sarautar Zazzau shekara dari ke nan. Barebari sun yi mulki sau uku, Katsinawa sun yi sau biyu, sai kuma a dan kyale Mallawa su hau. Amma fa ra’ayina ne in kuma akwai mai sayen ra’ayin sai mu yi jinga. Ni mahaifina asalinsa bakano ne, mahaifiyata asalinta Katsina gidan sarautar Katsina, suka haife ni a kasar Zazzau. Ka ga idan zan yi son kai ne sai in ce a sake bar wa Katsinawa su yi mulki karo na uku. Amma a bar wa Mallawa. A tuna mun sunan bamallen ma? Af! Sunansa Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli Magajin Garin Zazzau.

Na yi nan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply