Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 28.09.2020

Taskar Guibi: 28.09.2020

232
1
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, shida ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.
1. Yau fa ashirin da takwas ga wata na ji ma’aikata na gwamnatin tarayya musamman bangaren ilimi wato su jami’o’i da foliteknik da kwalejojij ilimi da sauransu da ke da nasaba da ilimi na cewa ba su ga dalilin da zai hana su korafin har yanzun ba su ji dilin-dilin na wannan watan ba fa.
2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da cewa ba su ga dalilin da zai hana su ci gaba da korafin shekara daya, da kusan wata uku suna zaman jiran ariyas na sabon albashi da aka yi kari tun watan Afrilun bara ba fa.
3. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da cewa ba su ga dalin da zai hana su korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairu na wannan shekarar da muke ciki ba fa.
4. Talakan Nijeriya na ci gaba da korafin bai ga dalilin da zai sa yana cikin mulkin Baba Buhari za a ce daga daya ga watan gobe za a kara masa kudin zama a duhu ba fa.
5. Talakan Arewa na ci gaba da korafin bai ga dalilin da zai hana a kori manyan shugabannin bangarorin tsaro na kasar nan da suka bari ana ta kashe talakan arewa, da sace masa kudi ko kaddara, da kona masa muhalli, da tilasta masa rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira ba fa.
6. Wasu gwamnoni a arewa suna korafin ba su ga dalilin da zai hana idan an kama namiji ya yi wa yarinya karama fyade dandake shi ba fa.
7. Fadar shugaban kasa na korafin ba ta ga dalilin da zai sa jama’a su dinga yada jita-jitar an kai ruwa rana tsakanin shugaban kasa da Tibubu ba fa.
8. Oshiomhole na korafin bai ga dalilin da zai hana shi amincewa da rushe kwamitin gudanarwa na jam’iyyarsa ta APC, da yin biyayya ga jam’iyyar da shugaban kasa ba fa.
9. Obaseki yana korafin bai ga dalilin da PDP za ta mika masa takardar shaidar shi ya lashe zaben fid-da-gwaninta na fafatawa takarar gwamna na jihar Edo ya ki karba ba fa.
10. Sojojin sama na ci gaba da korafin ba su ga dalilin da zai hana su fadin sun kai farmaki mabuyan ‘yan kungiyar Boko Haram da ke jihar Barno ba fa.
11. Ban ga dalilin da zai hana ni bayyana cewa jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari bakwai da saba’in da tara a jihohi da alkalumma kamar haka ba fa:
Legas 285
Ribas 68
Abuja 60
Edo 60
Inugu 56
Delta 47
Ebonyi 42
Oyo 41
Kaduna 19
Ogun 18
Ondo 16
Imo 12
Sakkwato 11
Barno 9
Nasarawa 8
Abiya 5
Gwambe 5
Kabbi 5
Kano 4
Yobe 3
Ekiti 3
Oshun 2
Ban ga dalilin da zai hana in ce jimillar wadanda suka harbu zuwa jiya su 24,077, wadanda suka warke, 8,625, wadanda suka riga mu gidan gaskiya su 558, wadanda ke jinya su 14,894 ne ba fa.
Ban ga dalilin da zai hana ni a daidai nan cewa mu wayi gari lafiya ba fa.
Af! Ban ga dalilin da zai hana ni in yi korafin masara ta yi tsada ba fa. Kodayake ban ga dalilin da zai hana manomin masara darawa har kunne ba fa.
Is’haq Idris Guibi ne ba wani ba fa
A Kaduna Nijeriya ne ba wata kasa ba fa

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply