Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 29.06.2020

Taskar Guibi: 29.06.2020

315
0

Jama’a assalamu alaikum barkanmu da asubahim litinin, bakwai ga watan Zulkida, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. daidai da ashirin da tara ga watan Yuni na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai karbi rahoto daga kwamitinsa a kan kwaronabairos PTF don jin wanne mataki kuma shugaban zai sake dauka.

2. An kwaso ‘yan Nijeriya su dari uku da goma sha biyar daga Ingila.

3. Gwamna Masari na jihar Katsina ya dora laifin karuwar hare-hare kan talakan jihar Katsina ga aikace-aikacen ‘yan -sa-kai da ke harzuka maharan.

4. Dakarun soja sun ce sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka so kai wa Zamfara da Katsina..

5. Kungiyar Kare Hakkin Jama’a mai suna SERAP a takaice ta maka gwamnatin tarayya a gaban kuliya a kan rabon kayan agaji na kwaronabairos.

6. Jibi talaka zai soma biyan sabon kudin zama a duhu da za a tsuga masa, mu a yanzun haka da nake wannan rubutu wuraren karfe biyun dare babu wutar babu dalilinta. Haka muke yini da kwana babu wuta, idan an kawota to kyandir ya fi ta kumari.

7. Masu motocin haya sun ninka kudin shiga mota zuwa ko’ina da sunan kwaronabairos, kuma babu ka’ida ko daya da masu motocin ke kiyayewa da ita don kare fasinjan da suka tsuga wa kudin mota. Haka suke cusa fasinja kamar kifin sadin na gwangwani.

8. Ma’aikatan gwamnatin tarayya bangaren ilimi, sun soma gunagunin gobe watan Yuni zai mutu babu labarin dilin-dilin.

9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya, da kusan wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi har yau ba amo ba labari.

10. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

11. Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun ci karensu babu babbaka a Dembuwa kodayake an ce sojoji sun dan rage musu jin dadi cin karen, sun kai musu farmaki suka tarwatsa su. Sai dai da yake sun ji dadin naman karen ba kadan ba, sai da sojojin suka dan ji jiki kafin su iya tarwatsa su in ji wani ganau.

12. Babban mai shari’a na jihar Kogi Nasiru Ajanah ya riga mu gidan gaskiya sakamakon wani ciwon da aka ce ba a bayyana ba.

13. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari hudu da casa’in a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 118
Delta 84
Ebonyi 68
Abuja 56
Filato 39
Edo 29
Katsina 21
Imo 13
Ondo 12
Adamawa 11
Oshun 8
Ogun 8
Ribas 6
Kano 5
Inugu 3
Bauci 3
Akwa Ibom 3
Kogi 1
Oyo 1
Bayelsa 1

Jimillar wadanda suka harbu a kasar nan, dubu ashirin da hudu da dari biyar da sittin da bakwai. Wadanda suka warke dubu tara da guda bakwai. Wadanda suka riga mu gidan gaskiya dari biyar da sittin da biyar. Wadanda ke jinya dubu goma sha hudu, da dari tara da casa’in da biyar.

Mu wayi gari lafiya.

Gaisuwa da jinjina ta musamman ga fitaccen shahararren lauyan nan da ke zaman kansa a nan cikin garin Kaduna da aka fi sani da Barista El-Zubair, amma ainihin sunansa Abubakar Alzubair da ke da ofishinsa na lauya a A.H. Gamagira Road, daura da randar Kasuwar Bacci a Tudun Wadar Kaduna. Ga mai bukatar aikinsa, sai ya tuntube shi a 08022182546, ko 07039340884, ko 08069288041. Ko ta imel: gidanladanai@gmail.com Lauya ne kwararre ana yawan hira da shi a gidajen rediyo da talabijin a kasar nan, da a kasashen waje.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply