Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 30.01.2021

Taskar Guibi: 30.01.2021

130
0

Assalamu Alakkum barkanmu da asubahin Asabar, goma sha shida ga watan Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Janairu, shekarar 2021.

1. Fadar Shugaban Kasa ta ce sam babu gaskiya a bayanin da kungiyar TRANSPARENCY INTERNATIONAL I.T. a takaice ta yi, cewa wai rashawa ta kara ta’azzara a Nijeriya, har ta zama ita ce ta biyu a yankin Yammacin Afirka. Fadar ta ce kungiyar ta kawo shaida a gani in da gaske ne.

2. Gwamnatin Tarayya ta ce ta bankado wani shiri da aka yi na bata wa Shugaban Kasa Buhari suna da zubar masa da mutunci.

3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don nada sabbin hafsoshin tsaro da ya zabo.

4. Sojoji sun shirya wa Buratai faretin sallama da aikin soja, a jiya a Abuja, bayan shekara 40 yana aikin soja. Har da kaddamar da littafi na biyu da aka rubuta a kansa.

5. Saboda matsawa da kai wa ‘yan kungiyar Boko Haram farmaki har inda suke da sojojin Nijeriya ke ta yi a ‘yan kwanakin nan, wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da ke hannun kungiyar kusan shekara bakwai ke nan, har ma da wasu, sun samu sun tsero daga hannunsu.

6. Wasu kidinafas sun je gidan wani dan majalisar wakilai da ke jihar Sakkwato da talatainin dare, Abdullahi Balarabe, inda Allah Ya ba shi sa’a ya tarwatsa kan jagoran kidinafas din da bindiga, ya ci gaba da musu barin wuta suka ranta a na kare.

7. A karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, kidinafas sun kwashi fiye da mutum hamsin, bayan sun kashe na kashewa, da jikkata na jikkatawa, suka tilasta wa al’umomi da dama tserewa daga muhallinsu.

8. Gwamnatin Jihar Kabbi ta yi dokar yanke wa kidinafa hukuncin kisa, shi kuma refis (rapist) mai fyade, hukuncin daurin rai-da-rai.

9. Kwamitin Shugaban Kasa da ke yaki da kwarona, ya ce babu mamaki su tilasta kulle a jihohin Legas, da Abuja da Filato saboda yadda cutar ke ci gaba da habbaka a jihohin.

10. Matan da aka kwaso daga Saudiya zuwa gida Nijeriya, su 424, sun ce atabau ba su yarda a killace su ba, tare da nuna takardun shaidarsu na ba su yo tsaraba ko guzurin kwarona ba.

11. Wasu matasa sun ba Gwamna Yahya Bello na jihar Kogi wa’adin mako biyu, ko ya nuna sha’awarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan a 2023 ko ya ga fushinsu. Shi kuma ya ba su amsar su dukufa wajen shiga jam’iyyarsa ta APC.

12. Wasu bayanai na nuna sai an yi wa kowanne dan Nijeriya allurar rigakafin kwarona, kuma gwamnoni za a fara yi wa.

13. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

14. Mutanen kauyen Guibi, da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumat na yanzu, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari tun lokacin yakin neman zabe.

15. Sabbin harbuwa da kwarona sun kai 1,114 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 408
Abuja 95
Filato 90
Ondo 66
Kaduna 63
Oyo 56
Barno 46
Imo 42
Edo 41
Ogun 37
Ribas 31
Ekiti 25
Yobe 20
Kano 18
Akwa Ibom 18
Delta 15
Oshun 15
Kwara 11
Bayelsa 6
Nasarawa 6
Zamfara 4
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 128,674
Jimillar da suka warke 102,780
Jimillar da ke jinya 24,317
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,577.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Bayan Shugaban Kasa ya sa hannu a dokar daurin wata shida ko tara, ko duka biyun ga wanda duk aka kama ba ya sa takunkumi, ko bai wa juna tazara, da sauransu don kauce wa yada kwarona ko dauka, na lura shi Baba Buhari na ta karbar baki a fadarsa iri-iri, shi ba ya sa takunkumin, kuma ba ya ba da tazara. Kodayake yana da rigar kariya ba mai masa komai, amma shi ba ya tsoron kwarona ne? Af!! Ashe bakina da asuwaki. Na yi nan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply