Home Taskar Guibi Taskar Guibi 30.04.2020

Taskar Guibi 30.04.2020

116
0
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, bakwai ga watan Ramadan, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Afrilun 2020.
1. Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya na korafin sai suna ganin kamar ana raina Baba Buhari ta kin bin umarninsa. Suka ce in ba raini ba, ta ya tun wuraren 23 ga watan nan ya ce a hanzarta biyan ma’aikata, da malaman jami’o’i albashi saboda halin da aka shiga na kwaronabairos, amma yau watan ya kare gobe za a shiga watan Mayu ba amo ba labari? Suka ce in lokacin Obasanjo ne, wani ya isa Obasanjo ya ba da umarni a ki bi sai an ga dama?
2. Buhun shinkafa dari biyar kwastam ta kama da aka shigo da ita ta barauniyar hanya a Legas.
3. Ranar litinin mai zuwa za a bude bankuna da ofisoshi na ma’aikatu da ke fadin kasar nan, amma ban da makarantu. Za a bude tare da kiyaye sharuddan hana yaduwar cutar kwaronabairos a cikin jama’a. Su kansu ma’aikata da za su fita aiki ba kowa ne zai fita ba, akwai matakin albashi. Dokar tilasta kullen za ta dinga aiki daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe, kuma babu zirga-zirga daga jiha zuwa jiha.
4. Gwamnatin tarayya ta raba wa wasu jihohi ashirin da hudu naira biliyan arba’in da uku da kusan rabi tallafi daga Bankin Duniya.
5. Kotu ta yi watsi da bukatar belin Maina da ake zargin ya wawure wasu makudan kudi na fansho.
6. An mayar da almajirai guda dari da ashirin daga jihar Gwambe zuwa jiharsu ta Yobe.
7. A jihar Kaduna ‘yan sanda sun kama a kalla mutum dari takwas da tamanin da shida da suke zargin sun saba wa dokar hana yada cutar kwaronabairos, aka gurfanar da arba’in da takwas da ake zargin gaban kotu, da yawancinsu masu gidajen barasa ne, da shugabannin wuraren ibada. Har ila yau a jihar ta Kaduna a yankin Kafanchan an yi wa wani bulala goma, da daurin wata biyu saboda satar kwamfuta laftab/Laptop. Sannan a titin kwansitushan da ke cikin garin Kaduna an yi gobara a wasu shaguna kusan ashirin.
8. Kungiyar kwadago ta jihar Kaduna ta ce ba ta yarda da taba wa ma’aikata albashi da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ba, ko a mayar wa ma’aikata kudinsu ko su kai ruwa rana da gwamnati.
9. Ma’aikatan wuta na nan suna ci gaba da raba takardar a je a biya kudin wuta. Ba zan ce kudin zama a duhu ba tunda wasu unguwanni sun ce ba laifi su ana ba su wuta. Mu dai a tamu unguwar ko in ce yankin, kudin zama a duhu za a je a biya. Amma ai sun ce za su daga kafa ba yanka saboda halin da ake ciki. Shan wuta kyauta har tsawon wata biyu labarin ya zama na kanzon kurege.
10. Zuwa jiya da daddare da na kwanta bacci sabbi da suka harbu da cutar kwaronabairos sun kai 196 kamar haka:
Legas 87
Kano 24
Gwambe 18
Kaduna 17
Abuja 16
Katsina 10
Sakkwato 8
Edo 7
Barno 6
Ebonyi 1
Adamawa 1
Ya zama zuwa jiya da daddare mutane 1728 suka harbu, 307 suka warke, 51 suka riga mu gidan gaskiya. Sauran 1370 ke jinya.
Ga yawan da ke kowacce jiha da abin ya shafa:
Legas 931
Abuja 174
Kano 139
Ogun 50
Gwambe 64
Oshun 34
Katsina 40
Barno 39
Edo 37
Oyo 21
Kaduna 32
Bauci 29
Akwa Ibom 12
Kwara 27
Ekiti 8
Ondo 8
Delta 7
Ribas 7
Taraba 8
Inugu 3
Neja 2
Jigawa 7
Abiya 2
Zamfara 4
Binuwai 1
Anambra 1
Adamawa 2
Filato 1
Imo 1
Bayelsa 1
Kabbi 1
Ebonyi 1
Nasarawa 1
Yobe 1
Idan na yi kuskure a gafarce ni.
Mu yi sahur lafiya, mu yini lafiya, mu yi buda baki lafiya.
Af! Da yake a labaruna na jiya, akwai labarin ranar litinin za a soma kwaso ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje da suke bukatar dawowa. To wani abokina da ke Sudan ya ga rubutun nawa, ya kuma kira ni a waya neman karin bayani. Ya ce ya je kare kundin bincikensa na digirin koli ne sai ta ritsa da shi a can. Ya kammala komai ga guzuri ya kare gari ba nasu ba. An dauki bayanansu tuntuni za a kwaso su shiru. Ya ce su a can ma bai ji ana wani bayani a kan cutar kwaronabairos ba. Saboda haka yake kira ga hukumonin Nijeriya su agaza musu guzurinsu ya kare su kwaso su, kafin su kai ga galabaita ko wulakanta.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply