Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 30.06.2020

Taskar Guibi: 30.06.2020

280
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, takwas ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Yunin shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Yau watan Yuni ke karewa, gobe za a shiga watan Yuli, ma’aikatan bangaren ilimi na gwamnatin tarayya na korafin da alamu sai an shiga wani sabon wata ba dilin-dilin babu duriyarsa, maimakon ashirin da biyar ga wata da aka musu alkawarin ba za a dinga wucewa ba a lokacin yakin neman zabe.

2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na korafin shekara daya da kusan wata uku ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

3. Talakawa na korafin daga gobe za su soma biyan sabon kudin da aka kara na zama a duhu.

4. Manoma na korafin ga koshi ga kwanan yunwa. Ga damuna ga ba taki. Manoman wuraren gabashin Birnin Yero, da wuraren yankin Afaka, da sauran wasu sassa na jihar Kaduna, na son zuwa gona amma kidinafas na nan kusa da gonakin sun kasa sun tsare duk wanda ya je ya zama haja ta sayarwa.

5. Mutanen da aka raba su da gonakinsu da muhallansu, aka kashe na kashewa, aka jikkata na jikkatawa a wasu sassan kudancin jihar Kaduna, musamman Zangon Kataf, da Zankuwa, da Kauru da sauransu, na farin ciki da suka ji gwamnatin El-Rufai ta kafa kwamitin gano bakin zaren magance dadaddiyar kiyayyar da ke nan dayani, sai dai sun ce ba su ji an ambaci Hausawa da Fulanin Zankuwa ba.

6. Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin shimfida bututun gas da zai tashi daga Ajakuta da ke jihar Kogi, ya ratsa Abuja, ya raba jihar Neja, ya gitta ta nan jihar Kaduna, ya dangana da jihar Kano, zai kuma ci dala biliyan kusan uku ba ‘yan wasu mutsamutsa(2.8billion Dollars).

7. Kwamitin shugaban kasa na yaki da kwaronabairos ya mika wa shugaban kasa rahotonsa, inda daga gobe za a kyale ‘yan makaranta da ke ajin karshe na firamare, da karamar sakandare, da babbar sakandare, duk su koma makaranta saboda shirye-shiryen jarabawa. An kuma dage haramcin zirga-zirga daga wata jiha zuwa wata, amma ban da awannin kulle.

8. Sojoji tara ‘yan kungiyar Boko Haram suka kashe a harin da suka kai Dambuwa.

9. An rantsar da kwamitin rikon kwarya na APC na Mai Mala Buni, har Giadom ya mika musu ragama.

10. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da sittin da shida a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 166
Oyo 66
Delta 53
Ebonyi 43
Filato 34
Ondo 32
Abuja 26
Ogun 25
Edo 24
Imo 15
Bayelsa 13
Binuwai 12
Gwambe 11
Kano 11
Kaduna 11
Oshun 8
Nasarawa 7
Barno 5
Katsina 2
Anambara 2

Jimillar wadanda suka harbu 25,135
Wadanda suka warke 9,402
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 573
Wadanda ke jinya 15,158

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wasu na korafin a kamen masu fyade da ‘yan sanda ke yi, suna hadawa da wadanda su laifinsu ba fyade ba ne, suna lalatarsu ne da amincewar juna duk ‘yan sanda na hada su su ce namijin ya aikata fyade. Kamar wani da na ga an kama shi da sunan fyade, ya shaida wa manema labaru cewa shi fa ba fyade ya yi ba, budurwarsa ce shekarunta sun kusan ashirin da biyar, kuma da amincewar juna suke lalata ba tilasta mata ko fyade ya mata ba. Ya yi korafin ga ‘yan sanda sun tarkata sun dora masa laifin fyade. Masu korafin suka ce ya kamata a iya tantance da bambance fyade, da da mutum namiji zai samu karamar yarinya wata ma jaririya, ko babbar mace ya mata fyade da karfi da yaji ko ita mace ta samu dan yaro ko babba ta masa fyade da karfi da yaji, da kuma wadanda balagaggu ne,, namiji da mace suke lalatarsu da amincewar junansu wato zina.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply