Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 30.12.2020

Taskar Guibi: 30.12.2020

306
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha biyar ga watan Jimada Ula/Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 30 ga watan Disamba na 2020.

1. Majalisar Dokoki ta Kasa ta mika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kasafin shekarar 2021 don ya sa hannu ya zama doka.

2. Ana ci gaba da zargin Gwamnatin Tarayya da jefa rayuwar ‘yan Nijeriya cikin hadarin kamuwa da cutar kwaronabairos da gangan, saboda tilasta musu su je su bi cunkoso da cincirindo da turmutsitsin neman lambar shaidar dan kasa a wannan lokaci da gwamnatin ke ikirarin dawowar kwaronabairos.

3. Jama’a na ci gaba da cunkoso, da gwamutsuwa, da cincirindo da turmutsitsin layin neman lambar shaidar dan kasa, a wurare kalilan da aka ware a je a yi rajistar cikin kankanin wa’adi.

4. Dakarun sojan sama, sun ce sun kai farmaki muhimman wurare guda biyar na kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa, har da makwancin wadanda sojojin suka yi imanin su ne suka kai wa al’umomin kudancin jihar Barno da na arewacin jihar Adamawa a cikin ‘yan kwanakin nan hari. Sojojin sun ce sun kashe su da lalata musu kayan yaki har da na kakkabo jirgjn yaki.

5. Dakaru sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga kuma kidinafas su shida tare da ceto mutum ashirin da uku da suka yi kokarin kidinafin a wuraren Kurfi ta jihar Katsina.

6. Dakaru sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga kuma barayin shanu su tara, a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

7. Gwamnatin jihar Binuwai ta haramta duk wata sabga ta babur a kananan hukumomi biyu, Katsina-Ala da Ukum, don kawo karshen kashe-kashen manya da kidinafin dinsu da ake ta yi a wuraren.

8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i, duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.

9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, da wa’adinsa ke shirin karewa, ya je ya cika musu alkawarin da ya daukar musu a lokacin yakin neman zabe, na zai gyara musu gadar da ta karye idan sun zabe shi.

10. Daga watan Maris na shekarar nan zuwa zancen da nake yi da ku a halin yanzun, likitoci, da nas-nas, da jami’an dakunan gwaje-gwaje na asibitoci, da sauran wadanda ke aiki a asibiti har da masu shara, su 476 suka harbu da kwaronabairos a Abuja.

11. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 749 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 299
Filato 131
Kaduna 83
Abuja 74
Kwara 35
Sakkwato 26
Edo 18
Kano 17
Katsina 16
Delta 11
Nasarawa 10
Ondo 9
Bauci 9
Ribas 5
Akwa Ibom 3
Jigawa 1
Oshun 1
Ekiti 1

Jimillar da suka harbu 85,560
Jimillar da suka warke 71,938
Jimillar da ke jinya 12,356
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,267

Mu wayi gari lafiya.

Af! A jerin tsokacin da mutane suka yi a rubutuna na jiya, na Urwat Abdul-Azeez ne ya fi daukar hankalina kamar haka:

“Kindanafas da “yan bindaga na cin Karan su babu babbaka, a shekaran jiya bayan an tashi kasuwar kafur ta jihar katsina da misalin 8 na dare “yan bindiga suka bud’ema matafiya wuta da yin fashi, har sun kashe wani matashi (Mu’awuya Jafar MLF). Allah ya ji’kanshi da rahama.

Maganar ra’ayin wani kan juyin mulki, wallahi da za’a samu sojoji matasa masu Kishin ‘kasa su ham6are gwamnatin da ‘kudurin shawo kan rashin tsaro a ‘kasar nan, da nima ina goyon baya akan haka.

Allah yasa mu dace, amin”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply