Home Sabon Labari Taskar Guibi: 31.01.2020

Taskar Guibi: 31.01.2020

106
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, biyar ga watan Jimada Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin da daya ga watan Janairu na 2020.

1. Bayan ruwan korafe-korafe da kiraye-kirayen da ‘yan majalisar dattawa da ta wakilai suka yi a kan manyan hafsoshin tsaro na kasar nan saboda ci gaba da tabarbarewar tsaro, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani taro da manyan hafsoshin tsaron jiya a Abuja.

2. Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya leka fadar shugaban kasa sun yi kus-kus-kus ta wasu ‘yan mintoci da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

3. Majalisar Dattawa ta amince da nadin Obiora a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya.

4. Babbar shugabar hukumar kula da al’amuran ‘yan Nijeriya da ke kasashen ketare Abike Dabiri Erewa ta ce babu wani dan Nijeriya da ke kasar Caina/China/Sin da ya kamu da cutar da ta zame musu annoba a can CORONAVIRUS.

5. Masu ilimin kimiyya na duniya sun soma rige-rigen gano maganin cutar CORONAVIRUS.

6. Majalisar wakilai ta kira shugaban ‘yan sandan Nijeriya da na hukukar tsaro ta NSCDC su je su musu bayanin dalilan da suka sa jami’an tsaro da ke dauke da bindiga ke yawan bindige jama’a suna mutuwa suna cewa tsautsayi ni.

7. An kai wasu tagwayen hari na kunar bakin wake a Muna Lawanti da ke jihar Barno.

8. Kotu ta ba da belin Mohammed Adoke a naira miliyan hamsin, ta kuma ba da umarnin a kamo mata wani tsohon ministan mai Dan Etete, da shi ma ake zargin yana da hannu a wata badakala ta mai da ake kira MALABU OIL ta dala biliyan daya da ‘yan kai.

9. Yau da daddare Birtaniya za ta fice daga Kungiyar Tarayyar Turai.

10. Abin mamaki sun bar wutar ta kwana. Tunda suka kawo ta jiya bayan magrib ba su dauketa ba har yanzun karfe biyar da wasu mintoci na asubah. Haka nan sun kawota jiya da safe suka dauke da rana.

11. A nemi jaridar Leadership Hausa wacce za ta fito yau da safe, don karanta labarun da na rubuta a dandalina na soshiyal midiya, daga juma’ar da ta gabata, zuwa jiya alhamis.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply