Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 31.01.2021

Taskar Guibi: 31.01.2021

137
0

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, goma sha bakwai ga Jimada Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin da daya, ga watan Janairu, na shekarar 2021.

1. Akwai sabbin harbuwa da kwarona mutum 1,883 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 1040
Abuja 298
Anambara 86
Ribas 54
Taraba 45
Ogun 42
Oyo 40
Akwa Ibam 38
Sakkwato 30
Ebonyi 30
Imo 28
Kaduna 28
Oshun 27
Kano 21
Binuwai 19
Edo 17
Gwambe 15
Ekiti 9
Delta 8
Jigawa 3
Kwara 2
Bayelsa 2
Filato 1

Jimillar da suka harbu 130,557
Jimillar da suka warke 103,712
Jimillar da ke jinya 25,267
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,578

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu sabon dogari Kanal Yusuf Dodo, tsohon dogarin Mohammad Abubakar da tun shekarar 2015 yake masa dogari, za shi karatun neman karin girma.

3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da rajistar ‘ya’yan jam’iyyar APC a Daura ta jjhar Katsina.

4. Gwamnatin Tarayya, ta fitar da kudi, don raba wa matan karkara su dubu dari da ashirin da biyar, naira dubu ashirin kowacce.

5. Kidinafas sun yi kidinafin mutum 21 a hanyar Kaduna zuwa Kaciya/Kachia.

6. Wasu da ke zargin mutanen wani kauye da ke yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, na tare da kidinafas da sauran makasa, sun je kauyen sun kashe mutum goma sha biyu, yawancin mutanen kauyen sun gudu sun bar kauyen.

7. Jami’an tsaro sun ceto wasu mata biyu daga hannun kidinafas a yankin Gwagwada da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

8. Gwamnatin jihar Kaduna ta amince ajin JSS1, da JSS3 da SS3 na sakandare, na gwamnati da na masu zaman kansu, da wasu zababbun azuzuwan/ajujuwan firamare, su koma makaranta gobe Litinin, daya ga watan Fabrairu na wannan shekarar. Haka nan wasu ajujuwa na makarantun Islamiyya da makamantansu za su koma goben.

9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawarin zai gyara musu a lokacin yakin neman zabe.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wasu na tambayar sun ji Salim Is’haq Guibi a tashar Liberty/Libati. Tabbas can ya koma da aiki. Yanzun haka da asubahin nan ma, idan aka kunna tashar ta LIBERTY da ke Kaduna, za a ji shi. Zuwa yanzun ya yi aiki a:
i. Tashar rediyo ta Raypower
ii. Tashar rediyo ta Freedom
iii. Ya zauna a rediyo Nijeriya Kaduna
iv. Tashar rediyo ta Spider
v. Tashar DITV Alheri Rediyo
vi. Tashar Liberty.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply