Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 31.05.2020

Taskar Guibi: 31.05.2020

152
0

1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta rasuwar tsohon Manajan Darakta na Rukunin Kamfanin Mai Na Kasa Maikanti Baru Kachalla da Allah Ya yi wa rasuwa a juma’ar da ta gabata cikin dare, a matsayin babban rashi, tare da yi wa iyalansa gaisuwar ta’azayya. Ya rasu bayan wata jinya a wani asibiti da ke Abuja yana da shekara sittin a duniya.

2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin wakilan hukumar kanfanin mai na kasa, bayan karewar wa’adin tsofaffin.

3. Nijeriya ta kwaso ‘yan kasar nan su dari biyu da sittin da takwas da ke kasar Sin wato Caina zuwa gida Abuja.

4. Hukumar Zabe ta Kasa ta ce kwaronabairos ba za ta hana ta gudanar da zabukan da ke gabanta ba a halin yanzun.

5. A jihar Binuwai an gudanar da zaben kananan hukunomi jiya asabar.

6. Kotu ta hana ‘yan sanda ko waninsu, a jihar Kaduna ko Sakkwato sake kama malamin nan Yabo, da ake zargin ya yi wa’azin da bai yi wa gwamnan jihar Kaduna dadi ba, har aka kama shi, aka sake shi.

7. Likitocin nan da ake kira RESIDENT DOCTORS sun yi barazanar zuwa yajin aiki muddin gwamnati ba ta biya musu wasu bukatu nasu ba, da suka hada da wasu alawus na aikin kwaronabairos, da kayan kariya daga cutar da sauransu.

8. Kungiyar Likitoci ta Kasa NMA a takaice, ta bukaci gwamnatin tarayya ta tilasta gudanar da gwajin kwaronabairos a jihar Kogi tunda gwamna Yahya Bello ya tirje.

9. Jiya ma mun dandana kudarmu wajen NEPA, har zuwa yanzun da asubah ba wutar babu dalilinta.

10. Ana ci gaba da korafi a kan kashe talakawa da ‘yan bindiga ke yi a jihar Sakkwato, da Katsina, da Zamfara, inda har Sadiya Ministar Jinkai ta ba hukumomin da abin ya shafa umarnin su hanzarta su kai wa wadanda suka tsira daga harin jihar Sakkwato kayan agaji.

11. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan, su kuma ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata daya ke nan suna zaman jiran ariyas, ga albashinsu duk wata sai ya zo da gibi, wasu ma a wawulo yake zuwa.

12. Kungiyar Turai ta lallashi Donald Trump a kan zuciyar da ya yi har ya ce Amurka ta babe da Hukumar Lafiya ta Duniya, da ya zarga da gaza tabuka komai a kan kwaronabairos tun tana karama ba ta girma ba. Amurka ke ba da karon dala miliyan dari hudu ga hukumar ta lafiya a duk shekara. Ka ga idan Amurka ta ja baya, WHO din za ta shiga rudu.

13. Jiya kafin in kwanta bacci da daddare, akwai sabbin wadanda suka harbu da kwaronabairos su 553 a jihohi kamar haka:

Legas 378
Abuja 52
Delta 23
Edo 22
Ribas 14
Ogun 13
Kaduna 12
Kano 9
Barno 7
Katsina 6
Jigawa 5
Oyo 5
Yobe 3
Filato 3
Osun 1

Da ke nuna kowacce jiha tana da alkalumma kamar haka:

Legas 4,755
Kano 951
Abuja 616
Katsina 364
Edo 284
Oyo 280
Barno 271
Jigawa 270
Ogun 259
Kaduna 244
Bauci 204
Gwambe 156
Sakkwato 116
Filato 104
Kwara 87
Delta 80
Zamfara 76
Nasarawa 62
Yobe 52
Akwa Ibom 45
Osun 45
Ebonyi 40
Adamawa 38
Imo 34
Kabbi 33
Neja 30
Ondo 25
Ekiti 20
Inugu 18
Taraba 18
Bayelsa 17
Anambra 11
Abiya 10
Binuwai 7
Kogi 2 **
Kuros Ribas 0

Jimillar wadanda suka harbu 9,855
Jimillar wadanda suka warke 2,856
Jimillar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 273
Jimillar da suke jinya 6,726

Na sa wa jihar Kogi taurari ne saboda gwamnan jihar Yahya Bello, ya ce kago alkaluman aka yi aka jingina wa jihar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya da na rubuta korafin da wasu malaman kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya ke yi a kan yadda albashinsu ke ta yin gibi duk wata, wata ma’aikaciya a irin wadannan makarantu ta turo korafinta kamar haka:

“Mallam Guibi,Barka da kokari.
Game da namba ta daya a kan maganar korafin da wani baban Malamin kwalejin foliteknik yayi,ni ma zan bi sahun shi in yi nawa korafin saboda da na ga dilin dilin jiya, nawa albashin ya ragu da dudu,dubu har dubu goma sha tara da yan kai(19,000 plus).
A gaskiya ni ban gane wannan mulki na Baba Buhari ba,saboda a wanan halin rayuwar da muke ciki a yanzu idan har Gwamnati bata Kara mana albashi ba to gaskiya tsakani da Allah bai kamata ta rage mana ba.
An ce an bamu minimum wage amma maimakon albashin mu ya karu sai raguwa yake tayi,sun bamu da hannu dama sun karbe da hannun hagu da sunan haraji.
Misali yanzu tun Feb IPPIS ki cire mani dubu hamsin da uku(53,000) da sunan haraji.
Uwar me Gwamnati tarayya ta ke mani? da za su rinka cire man wanan uban kudin.sa’anan kuma suna zabge mana kudi da sunan National Housing Fund.
Ni sai in ce zalunci ne kawai.
Ya kamata wanan Gwamnatin na Baba Buhari su gyara ko kuma mu dinga yi musu Allah ya isa”

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply