Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Karanta Labarai da Sharhi A Takaice 08.11.2019

TASKAR GUIBI: Karanta Labarai da Sharhi A Takaice 08.11.2019

76
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da takwas ga Nuwamba, na 2019.

1. Gwamnatin tarayya ta ba da hutun ranar litinin domin bikin Mauludi, na waiwayowar ranar goma sha biyu ga watan Rabiyul Awwal, da aka haifi cikamakin Annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W.

2. Hukumar kwastam ta dakatar da gidajen mai da ke da nisan kilomita ashirin da kan iyakokin/bodojin da aka rufe na kasar nan daga sayar da mai ko gas.

3. Hukumar yaki da rashawa ICPC ta ce zuwa yanzun gwamnatin tarayya ta yi nasarar kwato dukiyar jama’a ta naira biliyan dari biyu da take zargin wasu rikakkun gafiyoyin kasar nan sun wawura.

4. Hukumar tsaron farin kaya da aka fi sani da sibildifens ko NSCDC ta ceto mutum takwas daga hannun kidinafas, ta damke bakwai a Kaduna.

5. Sojoji da ‘yan I.S. da ke da nasaba da kungiyar Boko Haram sun yi kare jini biri jini, a wata karawa da suka yi a yankin jihar Barno. Yanzun dai sojojin ne ke bin su, har inda suke, su kai musu goron yaki, ba zama suke yi, suna jiran ‘yan kungiyoyin su kai musu farmaki, sannan su kare kansu ko mayar da martani ba.

6. Sojojin sama sun fatattaki wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da suka yunkura don kai hari shalkwatar ‘yan sanda da ke Damaturu.

7. Kotu ta dage shari’ar Abdulrasheed Maina har sai ashirin da daya, da ashirin da biyu ga wannan watan. An dai kai shi kotun a keken marasa lafiya.

8. Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Rochas Okorocha a matsayin sanata, da zaben Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

Mu yi juma’a lafiya.

Af! Wai yaushe rabon da mu kwana da wutar lantarki a Kinkinau Kaduna? Ai ya fi shekara. Wai yaushe rabon da mu ga ruwan famfo a Kinkinau ? Ai ya fi shekara. Wai shekara nawa da gwamnati ta lalata asibitin Amina Namadi Sambo da ke Kinkinau? Ai ya kai shekara uku. Wai shekara nawa gwamnati na mana alkawarin gyaran titin Kinkinau? Ya haura shekara goma. Tirkashi!

A nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fito yau juma’a don karanta rubuce-rubucen da na yi a fesbuk daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply