Home Labarai Taskar Guibi: Karanta labarun duniya a takaice

Taskar Guibi: Karanta labarun duniya a takaice

107
2

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha tara ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyu ga Yulin 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin sai an hukunta wadanda suka kashe mutum talatin da bakwai a jihar Sakkwato.

2. Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa da Femi Falani sun bukaci shugaban kasa ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi a kan matsalar tsaro da yadda kan kasar nan ya kama hanyar rarrabuwa.

3. Mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo-Agege ya jajanta wa gwamnati da mutanen jihar Delta saboda mutuwar mutum hudu sakamakon faduwar wani gini. Sai dai na ji wasu na cewa wadancan mutanen hudu suka dame shi, ba talatin da bakwai da aka kashe a jihar Sakkwato ba. Kuma ya kamata majalisar dattawa ta yi tsit na minti daya kamar yadda ta yi wa Funke. Osibanjo ya je Sakkwato kamar yadda ya yi wa Funke. Jonathan ya je Sakkwato kamar yadda ya yi wa Funke. Majalisar wakilai ta ce wani abu a kan mutanen na Sakkwato kamar yadda ta yi wa Funke. Atiku Abubakar ya ce wani abu kamar yadda ya yi wa Funke. Shugaban ‘yan sanda ya yi wani abu kamar yadda ya yi a kan Funke. Wole Soyinka da su Obasanjo a yi turanci da rubuta wasika a kan mutanen Sakkwato kamar yadda aka yi wa Funke. Buhari dai ya wanke kansa tunda ya ce wani abu a kan mutanen na Sakkwato.

4. Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu turawan Turkiyya su hudu a wata mashaya da ke jihar Kwara.

Daga

Is’haq Idris Guibi
Kaduna, Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

2 COMMENTS

Leave a Reply