Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Karanta Takaitattun Labaru na yau 25.10.2019

TASKAR GUIBI: Karanta Takaitattun Labaru na yau 25.10.2019

80
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da shida ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyar ga Oktoban 2019.

  1. Nijeriya ta mika wa Majalisar Dinkin Duniya ofishinta da ta gyara mata na Abuja, bayan kusan shekara takwas da kungiyar Boko Haram ta kai masa hari, har ya ragargaje, har mutane a kalla ashirin da uku suka mutu a ginin. Sun kai hari ginin ne a watan Agusta na shekarar dubu biyu da goma sha daya, inda tun lokacin Majalisar ke rabe-rabe a Abuja, har zuwa jiya da gwamnatin Nijeriya ta gama gyara mata ta kuma mika mata.
  2. Babban Bankin Duniya ya yaba cewa tattalin arzikin Nijeriya na cikin wadanda suka fi habbaka a baya-bayan nan a duniya, kuma mafi sauki da dadin walwalar kasuwanci idan aka kwatanta da can shekarun baya.
  3. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce kudin da aka ware wa ‘yan sanda a kasafin shekarar 2020, in sun zuba kudin bangaren gyaran motocinsu na sintiri kawai, cikin wata hudu sun kare. Ya bayyana haka ne a wajen kare kasafin ‘yan sanda a gaban kwamitin majalisar dokoki ta kasa.
  4. Hukumar EFCC ta kuma gurfanar da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Maurice Iwu a gaban kotu, saboda tuhumar ya wawuri wata naira biliyan daya da ‘yan kai daga watan Disamba na shekarar 2014 zuwa Maris na 2015.
  5. An daga shari’ar tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da ake zargin ya wawuri wata naira biliyan biyu, saboda rashin halartar alkali Abdullahi da ke shari’ar.
  6. ‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun ce sun kama mutum arba’in da bakwai da suke zargi da kidinafin, da sauran laifuka daban-daban.

Mu yi juma’a lafiya.

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe domin karanta rubuce-rubucen da na yi a fesbuk daga juma’ar da ta gabata, zuwa jiya alhamis. Godiya ta musamman ga babban editan jaridar Albulrazak Yahuza Jere, da editan jaridar Dutsen Kura Communication Limited DCL Zahradeen da shi ma yake buga rubutun nawa kullum a jaridarsu, sai babban editan Arewa DailyPost Ibrahim Ammani da rubutun nawa ke zama sharhin dandalinsa a kullum, sai su Bello Falama, da saurin dinbin masoya da na sani da wadanda ban sani ba, har da gidajen rediyo da ke daukar fassarar da nake yi wa labaru su watsa, ni Is’haq Idris Guibi, ke cewa ina godiya kwarai da gaske Allah Ya kare Ya kuma bar zumunci Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply