Home Sabon Labari Taskar Guibi: Karya Kumallo Da Labarai Da Sharhi A Takaice 13.09.2019

Taskar Guibi: Karya Kumallo Da Labarai Da Sharhi A Takaice 13.09.2019

69
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”enarookryb” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”wji0l2jfta” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”b2crsh7lno” animation_delay=”0″]

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha uku ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha uku ga Satumba na 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wa ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu babu sauran shan wahala. Korafe-korafe dai sun kara yawa na a lokacin da ya hau jiko na farko ya kara kudin mai, ga shi ya hau jiko na biyu ya kulle bodoji da kara kudin harajin tamanin kaya VAT daga kashi biyar zuwa kashi bakwai da ‘yan kai alhali karin albashi ya gagara. Kodayake ya umarci Ngige ya kafa wani kwamiti na sake tattaunawa a kan sabon albashin da kungiyoyin kwadago.
  2. Gwamnatin tarayya ta amince a kashe dala biliyan biyar da ‘yan kai don aikin dogo daga Ibadan zuwa Kano.
  3. Sojoji tara aka kashe, ashirin suka bace a wani hari na kwanton-bauna da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wa sojoji a Gudunbali da ke jihar Barno.
  4. Jami’an tsaro sun kama masu aikata laifuka daban-daban su wajen hamsin da biyar ciki har da kidinafas da suka yi kidinafin daliban nan na jami’ar Ahmadu Bello a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Har ila yau yaran Abba Kyari sun kama wani rikakken kidinafa.
  5. Ministan harkokin ‘yan sanda da shugaban ‘yan sandan Nijeriya sun yi wata ganawa ta sirri a Abuja.
  6. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce mutane dubu ashirin suka bace sakamakon rikicin Boko Haram a Arewa maso gabashin kasar nan.
  7. Wani lauya ya kai hukumar EFCC kara kotu yana bukatar ta biya shi naira biliyan daya saboda zargin ta bata masa suna.
  8. Hukumar kula da ayyukan Hajji ta kasa ta ce ta kammala dawo da dukkan alhazan Nijeriya gida.
  9. Nepa! Nepa!! Nepa!!! Baba Buhari ya ce ‘yan Nijeriya sun daina shan wahala ke nan. Anya Nepa za su yarda kuwa. Kai abin ya yi yawa.

Mu yi juma’a lafiya.

Af a nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe don karanta rubutuna da na yi daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis. Haka nan jaridar DCL Hausa, da kamfanin sadarwa na DCL wato Dutsen Kura Communication Limited da sauran kafofi daban-daban da jama’a na ci gaba da yada wadannan labarai da sharhi da nake yi kullum.
Hmmm! Sun kawo wutar yanzun karfe hudu da rabi da minti biyu na asubah. In ta dade ta kai karfe shida, sai kuma da rana, in ta dade awa biyu, sai kuma can wuraren karfe tara na dare, in ta dade ta kai karfe goma na dare. Allah Ya kyauta.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply