Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai A Takaice 10.12.2019

Taskar Guibi: Labarai A Takaice 10.12.2019

86
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha uku ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma ga watan Disamba, na 2019.

1. Talatar nan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Masar don halartar wani taro na ci gaban zaman lafiya.

2. Hukumar DSS ta aike wa kotun tarayya sakon neman ahuwa da ban hakuri saboda shiga harabar kotu da jami’anta suka yi don kama Sowore, shigar da ta saba ka’ida da kuma ja wa hukumar tofin – Allah- tsine.

3. Wole Soyinka ya ce kutsawar da jami’an DSS suka yi kotu don kama Sowore, rashawa ce ba karama ba, da kuma zubar da mutuncin bangaren shari’a a idon duniya.

4. Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani dandali na intanet da kowa zai iya ganin yadda kudade ke shiga da fita a kowacce hukuma da ma’aikata ta gwamnatin tarayya.

5. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya koka a kan matsalar wutar lantarki da ta ki ci, ta ki cinyewa a kasar nan.

6. An nada Muhammad Nami a matsayin sabon shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida FIRS bayan karewar wa’adin Fowler. Sai dai sai Majalisar Dattawa ta amince da nadin.

7. Kidinafas sun kashe mutum hudu a babban titin Abuja.

8. Sojoji sun ceto mata goma sha hudu, da yara goma sha bakwai daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Barno. Sun kuma kwato manyan makamai da kanana.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply