Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi 27.11.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi 27.11.2019

77
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da tara ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da bakwai ga Nuwamba, na 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zanta da Firaiministan kasar Dutch Mark Rutt, da kuma mataimakiyar babban shugaban Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed duk a Abuja.

2. Majalisar wakilai za ta gudanar da bincike a kan tashin hankalin da aka yi har da kisa a zaben gwamna na jihar Kogi da na jihar Bayelsa.

3. Sakamakon ci gaba da rufe boda hukumar kwastam na ci gaba da kama shinkafa da aka dura a manyan jarkokin manja, aka shafe bakin da manja, aka like da ledar manja don bad-da-bami, da kuma shinkafar da ake durawa cikin tankin man babur, da kuma a cikin tayoyin mota, da kuma motoci da harsashi ba ya iya huda su. Duk a lokacin da ake kokarin hauro da su kasar nan.

4. Hukumar EFCC ta damke babban shugaban gidan gyara hali na Kirikiri saboda zargin da ake masa na tabka wata badakala mai tsadar gaske.

5. Kotu ta ba da belin dan Abdulrasheed Maina, Faisal Maina a naira miliyan sittin, da sanya yau ashirin da bakwai don ci gaba da shari’arsa. Da ma an ba da belin mahaifin Faisal Abdulrasheed Maina a naira biliyan daya, tare da wasu tsauraran sharudda.

6. ‘Yan majalisar dokoki ta jihar Zamfara sun yi gyaran dokar da ta sa ake biyan wasu tsofaffin gwamnonin jihar naira miliyan goma a duk wata kowannensu. An ce tsohon gwamna Abdulaziz Yari na ta korafin an kwashe wasu watanni ba a ba shi wannan kudi ba. A yanzun gwamna Matawale ya ma sa a soke biyan ta wannan gyara da majalisar dokoki ta jihar ta yi.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply