Home Labarai Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 01.10.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 01.10.2019

103
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, biyu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da daya ga watan Oktoba, na 2019.

  1. Yau Nijeriya ke cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kanta, kuma anjima kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabi kai tsaye ta kafofin watsa/yada labaru. Tuni shugaban Amurka Donald Trump ya aiko wa da shugaban kasa Buhari sakon tayin murnar waiwayowar ranar samun ‘yancin kai.
  2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce an yi wadataccen tanadi na tsaro don jin dadin bikin ranar ta samun ‘yancin kai.
  3. Sojojin runduna ta bakwai da ke jihar Barno sun ce sun kama wani mutum da suke zargin shi ke samar wa ‘yan kungiyar Boko Haram kayan aiki. A dai jihar Barno a Gubio ‘yan kungiyar sun kai farmaki har suka ce sun kashe sojoji da yawa da kwasar ganimar kayan yaki. Sai dai sojoji sun musanta ikirarin na kungiyar, inda suka ce sun kai hari tabbas amma sojojin sun dakile su.
  4. Kotu ta bai wa DSS umarnin tsare Sowore.
  5. Wasu da suka fusata a Dutse Alhaji da ke Abuja sun kama wasu mutum uku, wata ruwayar ta ce mutum daya, da suke zargi kidinafas ne suka cinna musu wuta suka kone kurmus.
  6. Gobe laraba idan Allah Ya kai mu kotu za ta yanke hukunci a shari’ar Ganduje da Abba.
  7. Mutanen yankin Arewa maso gabashin kasar nan su wajen dubu arba’in suka gudu Nijar neman mafaka saboda rikice-rikicen yankin.
  8. Kidinafas sun sace mutum ashirin a Katsina, suka je Burkina Faso suka sayar da su a matsayin bayi.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply