Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 01.12.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 01.12.2019

80
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, hudu ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da daya ga watan Disamba, na 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin jami’ar nazarin al’amuran sufuri a Daura, aikin da zai ci dala miliyan hamsin.

2. Gwamnatin tarayya ta ce daga gobe litinin matafiya za su soma hawa jirgin kasa kyauta.
daga Legas zuwa Ibadan.

3. Hukumar kula da kare hakkin bil’Adama NHRC a takaice, ta nuna rashin amincewarta da dokar kalaman kiyayya a soshiyal midiya, da Majalisar Dattawa ke shirin yi.

4. Sojoji sun ceto mutum ashirin daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram din nan da suka kai hari Babban Gida da ke jihar Yobe a makon jiya. Haka nan sojoji a wani atisayensu na ‘Yancin Tafki, sun ragargaji ‘yan kungiyar Boko Haram da ke Arewacin Barno zuwa abin da ya nausa Nijar.

5. Jami’an imigireshen sun tarbe wasu mutane da suka yi safarar mutum ashirin da takwas suke shirin tsallake kasar nan da su.

6. ‘Yan sanda sun kama wasu matsafa goma sha shida a jihar Binuwai, da ake zargi da kashe-kashe a jihar.

7. Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar kula da kiyaye hadurra FRSC, suka kuma ji wa wasu mutane rauni a hanyar Lakwaja zuwa Okene.

8. Gwamnatin jihar Zamfara ta soke duk wani fili da aka bayar, ko ikon mallaka daga shekarar alif da dari tara da casa”in da tara zuwa yau.

9. A zaben da aka sake jiya a jihar Kogi, Smart yana da kuri’a dubu tamanin da takwas, da dari uku da saba’in da biyar, Dino Melaye yana da dubu sittin da biyu, da dari da talatin da uku.

 

Af! Ga wani sako da aka turo mun jiya a kan IPPIS da gwamnatin tarayya ke ta takaddama da malaman jami’a ASUU a kai:

Wasu officials na IPPIS suna amsar toshiyar baki don aringizon ma’aikatar bogi . Zai kyautu a bincika sosai ……Mubi Poly ……

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply