Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, uku ga watan Safar, shekarar 1441 bagan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyu ga watan Oktoba na 2019.
- Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari za shi Afirka ta Kudu don ziyara ta yini a kan hantarar da ‘yan can kasar ke yi wa musamman ‘yan Nijeriya.
- Fadar shugaban kasa ta ba da tabbacin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi tazarce ko neman tazarce ba, bayan wa’adinsa ya kare.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba gudu ba ja da baya a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da yaki da rashawa, da yaki da masu zambatar jama’a ta intanet, da kashe kudaden da ake samu a ta hanya mai kyau, da kuma sanya kafar wando guda da masu kalamai na haddasa kiyayya. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa al’umar Nijeriya jiya da safe na cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya.
- An gudanar da faretin bikin samun ‘yancin kai a farfajiyar fadar shugaban kasa da ke Abuja maimakon dandalin Igul/Eagle da aka saba gudanar da bikin. Wasu sun ce an yi hakan ne saboda matsalar tsaro, wasu suka ce an yi hakan ne don rage makudan kudin da za a kashe, ko tsimin kudin bikin maimakon almunbazzarancinsu.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Na kuwa ji kwastam na yi wa masu sayar da motoci a jihar Kaduna dirar-mikiya. A kan batun kudaden fito da sauransu.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
