Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi a Takaice 02.12.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi a Takaice 02.12.2019

82
0

Assalamu alaikum barkanmu da safiyar litinin, biyar ga watan Rabiul/Rabiul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyu ga watan Nuwamba, na 2019.

1. Babban lauyan nan Femi Falana, ya ce ya yi mamaki matuka yadda gwamnatin Nijeriya ta fi mutunta umarnin kotun masu jajayen kunnuwa da suka mana mulkin mallaka wato Ingila, fiye da umarnin kotunanmu na gida.

2. Hukumomin sojan Nijeriya sun ce babu gaskiya a labarin da wasu ke barbadawa a soshiyal midiya cewa hukumomin sojan na daukar tsofaffin mayakan kungiyar Boko Haram na musu yaki.

3. ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari al’umar Katarko, da ke jihar Yobe.

4. An sako DPO na ‘yan sanda da kidinafas suka yi kidinafin a jihar Adamawa, bayan ya kwashe wajen mako biyu a hannunsu.

5. Shugaban majalisar dokoki ta jihar Taraba Peter Dieh da shi ya fi kowa dadewa a majalisar ya sauka.

6. Kamar yadda ake zargin jami’an IPPIS na badakala a aikin da suke yi a kwalejin foliteknink ta gwamnatin tarayya da ke Mubi,, haka nan akwai zargin jami’an IPPIS da ke gudanar da aikin a FCE da ke Zariya, na cusa sunayen CONTRACT STAFF a cikin tsarin.

 

Af! Kamar yadda na yi bayanin ina shirin horas da ma’aikatan gidan rediyon firidom/freedom radio, har ila yau akwai shirye-shiryen zan horas da ma’aikatan Gidan Rediyon Nagarta nan gaba kadan.
Kamar yadda na sha nanatawa, na horaswa da ma’aikatan NTA, FRCN, KSMC, NewAge Network, DITV/Alheri Radio, Liberty Radio, daliban Kaduna Media Academy, da ma’aikatan KASU F.M. Radio, da dinbin dalibai da ke karatun aikin jarida a kwalejinmu ta Kaduna Foliteknik da sauransu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply