Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 03.10.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 03.10.2019

67
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis,hudu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta. Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da uku ga Oktoba na 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Afirka ta Kudu.
  2. Kotunan sauraron korafe-korafen zaben gwamnonin jihar Kano, da Sakkwato da Filato sun tabbatar wa Ganduje da Tambuwal da Lalong matsayin wadanda suka lashe zabukan jihohin nasu.
  3. Bayan kusan shekara hudu suna kulli-kurciya da Abdulrasheed Maina hukumar DSS ta ce ta kama shi, ta mika wa EFCC shi a wani zargi da ake masa na wawurar wasu biliyoyin naira, zargin da ya sha musantawa da neman a ba shi kariya ya fasa kwai.
  4. Gwamnatin tarayya na nan tana shirin maido da harajin bin manyan titunan kasar nan da aka fi sani da Toll Gate.
  5. Kungiyoyin kwadago NLC da TUC sun ce sun gaji da gafara-sa ba su ga kaho ba har yau. Saboda haka suka ba gwamnatin tarayya mako guda, wata ruwayar ta ce mako biyu ko dai ta kammala duk wani abin da ta ce ya yi saura na biyan sabon albashi, ko a tafi yajin aiki.

Jama’a mu wayi gari lafiya.

Af! Gaskiya masu manyan motoci na dandana kudarsu musamman a titin baifas na Namandi Azikiwe. Daga Unguwar Mu’azu zuwa Sabuwar Fanteka kusan kullum sai babbar mota ta lalace saboda lalacewar titin, titin ya cunkushe.

Af! Af!! Nepa ta tuna wutar ta koma ‘yar gidan jiya. Babu ita babu dalilinta sai sun ga dama.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply