Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 05.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 05.09.2019

60
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, biyar ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyar ga Satumban 2019.

1. An kama fiye da mutum dari da ashirin wajen yunkurin mayar da martani ko ramuwar gaiya ga kaddarorin Afirka ta Kudu da ke Nijeriya. Kamfanin MTN ya rufe sassansa da ke Nijeriya saboda tsoron harin na ramuwar gaiya. Tuni Nijeriya ta yi wa jakadanta a Afirka ta Kudu Kabiru Bala kiranye ya dawo gida, Nijeriya ta kuma fice daga wani taron tattatalin arziki na duniya a Afirka ta Kudu.

2. An ce ana shirin sabuwar tattaunawa a kan sabon albashin da ya gagara biya, tsakanin ministan kwadago Ngige, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban kasa Buhari.

3. Wasu ‘yan sanda uku tare da wasu da suke zargi da aikata laifi da suka kamo sun yi hadarin mota duk sun rasu bayan motar da suke ciki ta kwace wa direbanta a jihar Taraba.

4. A kokarin rage ayyukan makasa da sauran manyan laifuka, bangaren tsaro na jihar Kaduna ya haramta sanya shingen binciken ababen hawa a hanyar Kaduna zuwa Zariya, da Hanyar Kaduna zuwa Abuja, da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Har ya ba matafiya shawarar ka da su ba da hadin kai in sun ga irin wannan shinge, su kuma hanzarta kiran 09034000060 ko 08170189999. Ai kuwa jiya na fito Zariya wuraren karfe biyu na rana zan shigo Kaduna na ga wasu ‘yan sanda sun sa shingen bincike har da bindiga da sanduna da motarsu suna ta tare motoci suna karbar… Af! Bakina da goro.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Rabonmu da wuta tun jiya da safe, bayan mun kwana babu ita. Bayan sun kawo da safe ba ta dade ba suka dauke. Haka muka yini, muka kwana zuwa yanzun karfe hudu da rabi na asubah da nake wannan rubutu babu wutar. Ranar laraba ta makon jiya na sayo kati na naira dubu daya wato 36 na digo ko ma’anunin wutar wato 36 units. Jiya laraba kwana bakwai dai-dai, da suka kawo da safe na leka mitar na ga 31. Wato saboda rashin kawo wutar na ci 5 a kwana bakwai. Da ke nuna katin naira dubu daya na kai mun kusan wata biyu. Duk wata ana ba ni wutar naira dari biyar ina sha ke nan. Ka ga in ba ka da irin mitata ta iya-kudinka-iya-shagalinka, aka ce ka biya naira dubu biyar ko shida ko bakwai a wata an cuce ka. Shi ya sa kullum NEPA ke leken gidana ko na bi ta barauniyar hanya ne, da tuhumata ina sayen katin dari biyar. To katin naira dari biyar ke mun wata daya laifina ne?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply