Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 05.11.2019

TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 05.11.2019

83
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, bakwai ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyar ga Nuwamban 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan wani kudiri da ake ce masa DEEP OFFSHORE ACT, ya zama doka, da tana soma aiki dalolin da Nijeriya ke samu daga bangaren mai da gas za su yi matukar kara auki.

2. Gwamnatin tarayya ta fadi sharuddan da dole a kiyaye su a game da rufe kan iyaka da ta yi.

3. Kungiyar malaman jami’a ASUU shiyyar Fatakwal, ta ce har yanzun ba ta amince da IPPIS da gwamnatin tarayya ta bullo da shi ga dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya ba. Sai dai su malaman kwalejojin foliteknik ASUP su sun mika kai ana nan ana shigar da su.

4. Kungiyar kare hakkin jama’a da bunkasa tattalin arziki SERAP a takaice ta bukaci a binciki kudaden da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ke kashewa.

5. Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce dole gwamnoni su biya mafi karancin albashi ko a tsige su.

6. Kotu ta rushe zaben Alhassan Ado Doguwa ta ba da kwana casa’in a sake wani zaben a mazabarsa.

7. Kotu ta tabbatar da zaben Sanata Aliyu Magatakarda Wamako.

8. Mutum takwas suka shiga hannu a Legas a lokacin da sojoji suka dakile wani yunkuri na kai hari da kungiyar Boko Haram ta yi.

9. Mutanen Rigasa sun yi zanga-zanga kan yawan yi musu kidinafin jama’a a Rigasa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wani abokina ne jiya da muka hadu yake cewa “Guibi kana kokari wajen yi wa gwamnati cakulkuli a rubuce-rubucenka, sai dai ba ka yin adalci saboda ban taba ganin ka yi wa inda kake aiki cakulkuli ba ko kana nufin ku a wajen aikinku ba a aikata ba dai-dai ba?” Sai na ba shi amsar cewa … Af na tuna bakina da goro! Wutar lantarki ta kasa zama.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply