Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 07.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 07.09.2019

83
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, bakwai ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da bakwai ga Satumba, na 2019.

1. Geofrey ministan kula da al’amuran wajen kasar nan ya ce duk da abin da aka yi wa ‘yan Nijeriya a Afirka ta Kudu, Nijeriya ba za ta yanke hulda da kasar ba, sai dai dole a biya ‘yan Nijeriya barnar da aka musu.

2. A gida Nijeriya kuwa babban hafsan hafsoshin mayakan sama na kasar nan Sadique ya bai wa sojoji shawarar su karfafa yin atisaye a hanyar Kaduna zuwa Abuja, da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari don ci gaba da maganin kidinafas da bandis da ke addaba wadannan yankuna.

3. Da yake na tabo batun tsaro wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai wa ayarin gwamnan jihar Barno farmaki.

4. Da yake na tabo farnaki na ‘yan kungiyar Boko Haram, ‘yan kungiyar ISWAP da ke da nasaba da kungiyar ta Boko Haram ta kashe sojoji uku da dan sanda a jihar Barno.

5. A dai batun na tabbatar da tsaro hukumar kula da shige da fice ta bai wa baki ko wadanda suka zo kasar nan ci-rani kwana casa’in su yi rajistar zama a kasar nan.

6. Da yake na yi batun ‘yan ci-rani ‘yan majalisar dokoki ta jihar Legas sun ce ba su so aka saki ‘yan jihar Jigawa su fiye da dari da aka kama da babura sun shiga jihar ci-rani/acaba kwanakin baya ba.

7. Ita jihar Zamfara don hana nata mutanen tururuwa zuwa Legas ta mayar da malaman makaranta su dari biyar da hamsin da shida da ba a ga sunansu a takardar biyan albashi ba, bakin aiki.

8. Karo na biyar ke nan ana sace mun takalmi a masallacin Zamfara rod da ke Kinkinau.

9. ‘Yan Nijeriya na ci gaba da biyan kudin zama a duhu a wasu sassan kasar nan.

10. Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara casa’in da takwas a duniya.

 

Is’haq idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply