Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 07.11.2019

TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 07.11.2019

88
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, tara ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da bakwai ga Nuwamba na 2019.

1. Fadar shugaban kasa ta ce babu wata baraka ko rashin jituwa ko zaman doya da manja tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Osinbanjo kamar yadda wasu suke ta shaci-fadi a kai.

2. Mataimakin shugaban kasa Osinbanjo ya shugabanci zaman majalisar zartaswa ta kasa da ta saba yi a duk laraba.

3. Majalisar Dattawa ta yi wa kudirin dokar hana cin zarafin mata a makarantu karatu na biyu. Sai dai mata sanatoci da suka tofa albarkacin bakinsu a mahawarar sun ce ba fa a makaranta kadai ake neman lalata da mata ba, har ma a gidaje, da ma’aikatu, da ko’ina da ake mu’amala ta maza da mata, ko ta maza zalla, ko ta mata zalla.

4. Lauyan Sowore ya ce sun cika sharuddan ba da belin Sowore.

5. Kungiyar lauyoyi ta tilasta alkalai kaurace wa zaman kotuna a jihar Edo saboda yadda kidinafin alkalai ke kokarin zama ruwan dare.

6. An ba kamfanonin raba lantarki da ke da suna shigen na ‘yan rawar banjo wato Discos, nan da bakwai ga watan gobe, su kare lasisinsu na raba wuta, ko kuma…

7. Mutanen kasar Chadi/Cadi sun yi korafin rufe boda/kan iyaka da Nijeriya ta yi, ta sa komai ya yi tsada a kasarsu ta Cadi saboda komai nasu da Nijeriya suka dogara.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Muna idar da sallar la’asar jiya sai ga wayata tana girgiza don na kashe gunjinta saboda sallah. In duba sai na ga Garba Aliyu. Na mike na fita na amsa.
“Malam Guibi ya aiki? Rediyon Faransa wato RFI (Radio France International) ke so ya yi hira da kai ta minti uku yanzun nan a matsayinka na daya daga cikin wadanda ke kan gaba wajen sayen DATA, saboda wa’adin kwana biyar da minista Pantami ya bayar na kamfanonin sadarwa su rage kudin”
Nan take na amince a kofar masallaci muka yi hira ta minti uku ya nada, karfe biyar na kamo tashar na ji ya cilla hirar. Godiya ta musamman ga Garba Aliyu, har ila yau godiya ta musamman ga Ibrahima Yakubu da ke yawan cilla ni sashen Hausa na rediyon Jamus, sai Zahradeen Umar Dutsen Kura da ke yawan cilla ni sashen Hausa da na turancin Ingilishi na rediyon Jamus, wanda har ila yau shi ya hada ni da Salihu Adamu Usman da Sumaiya Ibrahim Yusuf na BBC Media Action, su kuma suka soma cilla ni a BBC Hausa. Sai rediyo da talabijin na gida kamar su Fatima Kuta da Ahmed Kudan da ke cilla ni a NTA, sai Musa Idris Barnawa, da Kabir Kusfa, da Lawal Kaya, da Ummu Sadiqah, da ke cilla ni a rediyon Nijeriya na Kaduna, sai Dahiru Ahmad da Najib Tsafe da ke cilla ni a rediyo da talabijin na Liberty, sai Zakari Aminu da ke cilla ni a rediyon freedom, sai Suleman Dangaye, da Mai Ismi, da MC Arewa, da Shehu Shagari Rigasa da Umar Ridwan da ke yawan cilla ni a DITV da alheri rediyo, ba zan manta Aminu TC da Mustapha na KSTV da Capital TV ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply