Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 08.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 08.08.2019

75
0

Assalamu alakum barkanmu da asubahin laraba, shida ga Zulhijja/Zulhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da bakwai ga Agustan 2019.

1. Ranar ashirin da daya ga watan nan na Agusta shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da sabbin ministoci.

2. Gwamnatin tarayya ta ba da ranar goma sha biyu, da goma sha uku ga watan nan na Agusta su zama ranakun hutu domin babbar Sallah. Har na tuna wuraren shekarar 1997 da na soma aiki da gwamnatin tarayya, idan Sallah ko kirsimeti ta kasance za a yi ta wuraren goma ga wata, muna samun albashin wannan watan. Misali a yanzun za a biya mu albashin watan nan na Agusta don mu ji dadin hidimar Sallah. A yanzun kuwa ina! An daina kodayake wasu jihohin sukan biya, ko su ba da rabin albashi kyauta ko bashi.

3. Ma’aikata manya da kanana na jami’o’i wato NASU da SSANU da suka sha alwashin durkusar da jami’o’in kasar nan, in gwamnatin tarayya ba ta biya su alawus na EARNED ALLOWANCE ba, sun soma boren saboda sun ji shiru, da

4. PDP ta nemi gwamnatin tarayya ta saki fursunoni na siyasa har da SOWORE shugaban boren juyin-juya-hali. Kotu ta ba da belin shida daga cikinsu da aka kama, zuwa gobe takwas ga watan nan za ta san matsayin Soworen.

5. EFCC na kokarin samun umarnin kotu don dode duk wata ajiya ta banki ta jihar Bauci.

6. Mutanen yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun ci gaba da kokawa a kan kashe mutane, da sace na sacewa, da ji wa na ji wa rauni, su kansu jami’an tsaro ba su tsira ba, da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi.

7. An rufe jami’ar Tafawa Balewa da ke Bauci, sakamakon wata ambaliya da ta yi sanadiyyar karyewar wata gada, da mutuwar dalibai hudu.

8. A jihar Ondo wasu ‘yan fashi sun auka banki har suka kashe mutum guda.

9. Koriya ta Arewa na ci gaba da cilla makamai masu linzami.

Mu yini lafiya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply