Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 09.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 09.08.2019

77
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, bakwai ga watan Zulhijja/Zalhaj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da takwas ga Agustan 2019.

1. Ana nan ana takaddama tsakanin sojoji da ‘yan sanda a kan zargin wasu sojoji sun bindige wasu ‘yan sanda uku da farar hula daya har sun mutu a Taraba, su kuma sojoji suka ce an kira su a waya su agaza ga kidinafas nan sun sato wani, suka tare hanya, har wurare uku suka ki tsayawa da wata mota fara kirar bas, da suka zo waje na uku ne suka bindige hudu, tunda sun ki tsayawa, wasu suka ranta a na kare. Sojojin suka ce sai daga baya ne ‘yansanda suka nuna musu katin shaidar su ‘yan sanda ne sun kamo wani rikakken kidinafa Hamisu cikin farin kaya ne, sojojin suka tare su. An ce a wajen rikakken kidinafan da suka kamo, ya tsere. Na ga tashar TVC News ta nuna bidiyon yadda lamarin ya auku a labarunsu na karfe goma na jiya da daddare. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin a gudanar da bincike.

2. Hukumar DSS ta kama wani da wata da suke yin sojan gona cewa shi mataimakin shugaban kasa ne, ita kuma Aisha Buhari ce.

3. Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta ce a watan jiya na Yuli, ta kama mutum saba’in da tara da take zargi da aikata laifuka daban-daban cikinsu har da wani soja da aka taba kora daga aiki.

4. Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da wata hukumar da za ta binciki rikicin Kajuru.

5. A hanyar Kaduna zuwa Abuja an bindige wani mai wa’azin coci babba, aka sace matarsa.

6. Mutanen yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna na ci gaba da neman agajin gwamnati a game da yadda tsaron rayukansu da na dukiyoyinsu ke neman gagara a yankin.

7. Jami’ar Bayero ta samu lasisin bude tashar talabijin, bayan na rediyo da take da shi.

8. A jihar Kogi majalisar dokoki ta jihar ta soma yunkurin cire mataimakin gwamnan jihar Simon saboda zargin yana ta kalamai a kafofin watsa labaru na cin mutuncin jihar da gwamnanta. Shi kuma ya ce don ya fadi gaskiya ana rashawa da badakala da kudin jihar ne, shi ya suka tsane shi..

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar da sharudanta guda bakwai a kan izinin da kotu ta ba El-Zakzaky da matarsa su je Indiya jinya. Gwamnatin ta ce in sun je dole su dawo ba za su nemi wata mafaka ta siyasa su ki dawowa ba, duk wanda zai je gaishesu sai an tantance shi, su za su yi komai na takardunsu da kudin tafiya da na jinya da kansu, dole wani basarake mai daraja ta daya a kasar nan ya tsaya musu, dole wani fitacce da ke da muhalli a Kaduna ya tsaya musu, dole su rubuta a rubuce alkawarin za su dawo, dole su nisanci wani abu da zai shafi shari’ar da ake musu a lokacin da suke can, da dai sauransu.

Af! Af!! Majalisar dokoki ta kasar Kenya ta kori wata mace ‘yar majalisar daga cikin majalisar saboda ta shiga majalisar tana shayar da jaririnta nono/ tana ba shi mama.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply