Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 09.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 09.09.2019

79
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, tara ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da tara ga watan Satumba na 2019 wato 9/9/19.

1. ‘Yan Afirka ta Kudu dauke da makamai sun sabunta korar baki da suke yi daga kasarsu. A yanzun suna nan suna ta kai wa baki farmakin su tarkata inasu-inasu su bar musu kasarsu. A watan gobe na Oktoba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuduri aniyar zuwa kasar.

2. Kungiyar kare hakki SERAP a takaice, ta bukaci kasashen Afirka su kai Afirka ta Kudu kara kotu.

3. ‘Yan sanda sun kashe kidinafas uku suka kama ashirin da suke zargi a jihar Kaduna, can ma a Kano sun ce sun kama fiye da mutum dari da suke zargi.

4. Hukumar kula da ayyukan hajji ta kasa ta ce babu gaskiya a labarin da ake ta yadawa cewa wai wani jirgin alhazai ya fado ko gamuwa da wata matsala wajen sauka a Minna ta jihar Neja.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A yanzun a awa/sa’a ashirin da hudu, muna samun wutar sa’a hudu ne kacal, sa’a ashirin babu wutar. A kawo karfe goma sha biyu na rana, a dauke karfe biyu na rana, sai kuma a kawo ta karfe takwas na dare, karfe goma na dare na yi sai a dauke. Haka ake yi kullum. Ka ga an matsa dole sai talaka ya biya kudin wutar awa ashirin da hudu, alhalin wutar awa hudu aka ba shi. Ina talaka zai kai kukansa? Babu. Baba Buhari dai af! Bakina da goro. Na yi nan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply