Home Sabon Labari TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 09.11.2019

TASKAR GUIBI: Labarai da Sharhi A Takaice 09.11.2019

73
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha daya ga watan Rabiul/Rabiyul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da tara ga watan Nuwamba, na 2019.

1. Bayan dai ta tabbata an sallami wasu mukarraban Osinbanjo, da dai sauransu har wajen su talatin da biyar, batun da mai magana da yawun Osinbanjo ya ce ba a aikata ba, shaci-fadi ne na ‘yan soshiyal midiya, shi kuma Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ya gaskanta ba shaci-fadi ba ne, fadar ta shugaban kasa ta ce an rage su ne, saboda rage kudin da ake kashewa bangarensu, kuma kusan ma a yanzun ba su da wani aikin da suke yi. Fadar ta jaddada cewa babu wani zama na doya da manja da ake ciki tsakanin shugaban kasa Buhari da Osinbanjo.

2. Femi Falana, lauyan Sowore, ya yi barazanar zai kai hukumar tsaro ta DSS kara kotu saboda, duk da sun cika sharuddan ba da beli, DSS na ci gaba da tsare da shi.

3. Majalisar Wakilai ta goyi bayan Majalisar Dattawa a kan tilasta wa jami’ar Maiduguri rage kudin makaranta da ake zargin ta tsuga wa dalibai.

4. Gwamnatin tarayya ta amince ta kara tsawon wa’adin da ta bayar na sanya ma’aikatan da suka yi saura cikin tsarin IPPIS. A da ta ce duk wanda ba a sa shi a wannan watan ba, ba shi ba albashin watan. A yanzun har sai watan gobe.

5. Ana gudanar da taron kasashen yammacin Afirka don gano bakin zaren yadda za a magance matsalar wutar lantarki da ke addabar yankin. Yanzun ma haka da nake wannan rubutun karfe biyar saura minti shida na asuba ba wutar, kuma haka muka kwana babu ita.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply