Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 10.10.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 10.10.2019

81
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha daya ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitra, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai ga goma ga Oktoban 2019.

  1. Labarin da na lura yake ta karakaina jiya kuma ake ta turo mun shi, shi ne na cewa babu mamaki gwamnatin tarayya ta karbe lasisin wasu kamfanoni raba wutar lantarki da aka fi sani da sunan ‘yan rawa wato DISCOs na wasu jihohi har da na Kaduna saboda gazawar da suka yi bangaren raba lantarkin.
  2. Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago za su kammala tattaunawa a kan karin albashi ranar sha biyar ga watan nan na Oktoba.
  3. ‘Yan Majalisar Dattawa da na Wakilai sun soma muhawara a kan kasafin kudin 2020 suke kuma sa ran amincewa da shi ranar ashirin da takwas ga watan gobe wato Nuwamba.
  4. ‘Yan sanda sun kama wadanda suka kashe babbar hafsan sojar nan ta ruwa a Kaduna.
  5. Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a jihar Filato, kidinafas suka sace wani fasto a jihar Nasarawa.
  6. Tsofaffin ministocin gwamnatin soja ta Janar Buhari sun kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar jiya karkashin jagorancin tsohon ministansa na waje Farfesa Gambari.
  7. Bangaren tsaro da ya binciki kyaftin din nan na soja da wasu sojoji da suka kashe ‘yan sanda suka saki rikakken kidinafan nan Hamisu a jihar Taraba, ya nemi a hukunta duka sojojin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply