Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 12.09.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 12.09.2019

70
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”2cne8qb3z” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”ex8efiy7k” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”h6823ghm8l” animation_delay=”0″]

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha biyu ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha biyu ga Satumban 2019.

1. Jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi taron majalisar zartaswa na farko ajikon mulkinsa na biyu, tare da bayyana dalilan kirkiro karin ma’aikatu da bai wa sabbin ministocin da ya nada shawarar su bai wa marada kunya.

2. Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP za su daukaka kara kotun koli saboda sun ce ba su amince da hukuncin da kotun kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke a jiya ba, na fatali da ilahirin korafe-korafen da Atikun da PDP su ka yi a kan zaben Buhari ba. Shi kuwa shugaban kasa Buhari cewa ya yi hukunci nasara ce ga ‘yan Nijeriya tare da bukatar duk wani mai ja ya hakura haka nan, ya zo a hada karfi don ciyar da kasar nan gaba.

3. Jiya da daddare wuraren karfe tara da rabi da wasu mintoci na dare jirgin rukuni na farko na ‘yan Nijeriya da ke Afirka ta Kudu ya iso Legas.

4. Sojoji a Kaduna sun yi kundunbala sun ceto wasu matafiya su bakwai mutanen Offa, da kidinafas suka yi kidinafin dinsu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Kwamanda mayakan sojan THUNDER Ibrahim Gambari ya ce yanzun kidinafas da ke kan hanyar za su kwashi tutunsu a hannu.
Har ila yau a Kaduna kungiyar kiristoci ta kasa ta ce an kashe wani fasto na cocin baftis.

5. A jihar Katsina bandis na ci gaba da sako mutanen da suka sace saboda sasantawar da suke kan yi da gwamna Masari, wasu kuma na ci gaba da kidinafin a jihar kamar yadda suka kai wa kantoman Matazu harin sace shi har gida da talatainin dare.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gaskiya yawancin hadurran da ke aukuwa a hanyar Kaduna zuwa Zariya da Zariya zuwa Kaduna ganganci ne na direbobi musamman masu manyan motoci, da masu sharon da ‘yan gwaf. Kowa yana yin tuki na son rai. Tuki na ganganci a tudu da kwari da kwana da mugun gudu da obatakin a kwana, ko ta dama ko ta hagu wato shoda. Masu manyan motoci sai su fada hannun da ba nasu ba takamar idan an yi karo mai karamar mota ne zai mutu. Ko babbar mota ‘yar uwarsu suka hango sai su auka obatekin, ga hanyar ta zama wanwe. Masu sauki-saukin tukin fitar hankali su ne ‘yan bas. Irin tsofaffin bas din nan na da. Amma gwaf da sharon da doguwar bas din nan etinsita, to sai fa a hankali in sun hango babbar mota na zuwa sai su auka obatekin, akan yi sa’a wasu masu manyan motocin na da hankali, sai ka ga sun kauce musu sun koma shoda.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply