Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 13.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 13.08.2019

64
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha biyu ga watan Zulhijja/Zulhaj, shekara ta 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha uku ga Agustan 2019.

1. Shek El-Zakzaky ya tafi Indiya jiya tare da matarsa ta tashar jiragen sama ta Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da wuraren karfe bakwai saura minti goma sha biyar na bayan almuru, a wani jirgin sama na kamfanin Emirate.

2. Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban kwalejin ilimi ta Binuwai.

3. Wani jami’in hukumar tsaron farin kaya da aka fi sani da NSCDC a takaice ya bindige wani dalibi farin kaya na jami’ar Neja Delta da ke jihar Bayelsa har ya mutu.

4. Hukumomin soja sun kori sojan da ya yi wa wata daliba fyade a jihar Ondo daga aiki, suka kuma mika wa ‘yan sanda shi, su kuma suke shirin gurfanar da shi a kotu.

5. Ana shirin bincikar wasu makudan kudi biliyoyi na samar da wutar lantarki da ake zargin an wawure tun daga lokacin gwamnatin Obasanjo, da su Abdulsalam, da ‘Yar Adua, zuwa Jonathan.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A ci gaba da shagulgulan Sallah lafiya, kuma gobe laraba ma’aikata za su koma bakin aiki bayan hutun Sallah da aka sha. Ba wanda ya kawo mun rago, na yi tayin gafiya an ki zuwa sai wata ce ta ce za ta ci amma matsalar gidana ya mata nisa.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nigeria.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply