Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 13.10.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 13.10.2019

78
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha hudu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha uku ga Oktoban 2019.

  1. ‘Yan sanda sun kama wasu mutane a Kano, da ke satar ‘ya’ya na goye su kai su Anaca/Onitsha da ke jihar Anambra su sayar da su daga naira dubu dari zuwa dubu dari da hamsin ga masu bukatar haihuwa ko yara na riko su kuma su canza musu suna da addini sun zama nasu. Zuwa kama su, sun saci yara tara sun kai Anaca an sauya musu suna da addini.
  2. Kwamitin da aka kafa a jihar Zamfara karkashin jagorancin tsohon shugaban ‘yan sanda Muhammad Abubakar, don bincike a kan kashe-kashe da satar jama’a a jihar, ya gano manyan sarakuna guda biyar, da kanana sun haura arba’in, da sojoji goma da ‘yan sanda da ma’aikatan gwamnati duk suna da hannu. Kuma daga shekarar dubu biyu da goma sha daya zuwa bana 2019 an biya kidinafas fiye da naira biliyan uku, ga marayu da aka kashe iyayensu, da mata zawarawa da aka kashe mazajensu ba iyaka.
  3. Mutanen yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun ce kusan kullum sai kidinafas sun yi kidinafin mutane, da kashe na kashewa, da tarwatsa kauyuka.
  4. Kidinafas sun sako shida daga cikin mutum tara da suka yi kidinafin a Abuja, sai dai waninsu ya ce sai da aka biya kidinafas din kudin da suka nema, sannan suka sako su.
  5. Kidinafas da suka yi kidinafin shugaban makarantar sakandare ta kere-kere da ke Mahadar Kajuru a jihar Kaduna sun yi ragi daga naira miliyan ashirin zuwa miliyan biyar.
  6. Sojoji sun kama wasu manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram su tara a karamar hukumar Goza da ke jihar Barno.

Mu wayi gari lafiya.

Af ga wani rubutu da na yi a ranar alhamis, goma sha uku ga watan Oktoba, na shekarar 2016, yau shekara uku dai-dai da ya zo dai-dai da zaman da ake ta yamadidi a kai, tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha. A karanta lafiya.

Jama’a barkanmu da asubahin alhamis tare da fatan mun wayi gari lafiya,kuma yau ma ina tare kai tsaye da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ranka ya dade barka da asubah ya shirye-shiryen tafiya Jamus?
“Malam Guibi mun gode wa Allah Mai kowa Mai komai”
Yauwa ranka ya dade ka yi hakuri yau zan dan shiga gidanka wato batun matarka Aisha ina ganin bai kamata tana yawan yin abubuwan da za su zubar maka da kima ba. Ka ga wancan karon ta fita kasar nan ta dinga yin shiga irin ta jahilan farko amma da yake ana sonka wannan ya wuce. To a yanzun ta je tana fada wa duniya batun da ku biyu a daki ya kamata ta fada maka ba ka ganin idan an bi ta barawo ya kamata a bi ta mabi sawu? Ina nufin a bincika watakila gidan da munafukai kai kuma babu mamaki ka ki ka saurareta ka san halin mata wasunsu ba mai iya musu sai Allah da Ya halicce su? “Hhhhh (ajiyar zuciya da dogon tunani) haka ne Malam Guibi ni ma lamarin yana daure mun kai amma zan tsawata kuma za ta daina”
Ranka ya dade idan ta ki daina keta maka rigar mutunci ina da wata bazawara idan kana so ita ma sunanta Aisha zan maka hanya idan ka aureta za ta dinga rufa maka asiri.
“Hahaha Malam Guibi kar fa ka bari Aisha Buhari ta ji ka ka san mata ba sa son kishiya” Ranka ya dade to ta yi wa bakinta takunkumi in ba ta son kishiya don duk mace mai tona asirin mijinta a titi sunanta mata-maza.
“To na gode Malam Guibi”
Ni ma na gode ranka ya dade a dawo lafiya. Jama’a mu yini lafiya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply