Home Sabon Labari Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 14.08.2019

Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 14.08.2019

60
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha uku ga watan Zulhijja/Zulhajj, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha hudu ga Agustan 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba babban bankin Nijeriya umarnin ya daina ba da kudaden musaya na kasashen waje ga masu safarar shigo da kayan abinci kasar nan.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar sansanin ‘yan gudun hijira da ke Batsari a jihar Katsina.

3. Hakimai goma sha daya sun bijirewa umarnin Ganduje na kada su je hawan da sarki Sanusi ya yi. Shi kansa Gandujen tare da shugaban kasar Guinea ya halarta. An kuma ce sarkin da gwamnan sun gudanar da abubuwa na al’ada da aka saba , ba kamar yadda ta kasance a karamar Sallah ba.

4. Sojojin sama sun murkushe wasu ‘yan kungiyar Boko Haram a Izza da ke jihar Barno.

5. Dalibai Tiv/Munci/Tibi na zargin Jukunawa sun kashe musu dalibai ‘yan uwa biyu da wani ma’aikaci.

6. Wata yarinya ‘yar shekara shida da aka yo kidinafin dinta daga jihar Bayelsa, aka biya kudin fansa naira miliyan daya, an gano ta a wani otel da ke nan Kaduna bayan ta kwana shida a hannunsu.

7. Wasu na korafin labarin albashi mafi kankanta/karanci ya yi nisan kiwo.

8. Yau ma’aikata za su koma bakin aiki bayan hutun Sallah da aka sha.

Mu wayi gari lafiya.

 

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply